Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna

Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna

  • Rundunar sojojin ƙasa ta Operation Save Haven ta samu nasarar dakile hare-haren yan bindiga da dama a Kaduna
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar
  • Yace aƙalla mutum 5 cikinsu harda yaro ɗan shekara 10 sun rasa rayuwarsu sanadiyyar harin

Kaduna - Akalla mutum biyar cikinsu harda karamin yaro ɗan shekara 10 suka rasa rayuwarsu yayin harin yan bindiga a yankin karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Wasu da dama sun jikkata a wani harin yan bindiga yayin da sojojin Operation Safe Haven suka fatattaki wasu hari a jihar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan sojoji sun dakile yunkurin wasu yan fashi na sace mutun biyu tare da kuɓutar da wasu shida a wurare daban-daban a karamar hukumar Jema'a, kamar yadda punch ta ruwaito.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i
Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kai hare-haren a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kwamishinan ya gargaɗi nutanen dake yankunan da lamarin ya faru cewa su zauna lafiya, kada su ɗauki doka a hannunsu.

Kwamishinan yace:

"Gwamnatin Kaduna na kara jan hankalin mutane su zauna lafiya su dakatar da tada rikici a tsakaninsu bayan mun samu rahoto daga jami'an tsaro cewa an kashe mutum 5 a wasu hare-hare da aka kai karamar hukumar Zangon Kataf."
"Rahoton ya nuna cewa an kashe karamin yaro ɗan shekara 10 a dajin Madauchi yayin da yake kiwon dabbobi, an gano gawar yaron kuma an birne ta."
"Hakanan kuma an kai wani hari Kurmin Masara kusa da Bakin Kogi, inda wani mutumi, Philip Magu, ya rasa ransa kafin daga bisani haɗakar dakarun soji da yan sanda su fatattaki maharan."

Yan bindiga sun sake kai wani hari na daban

Kara karanta wannan

Rikici a Plateau: An kashe mana mutum 70 cikin kwanaki 4, Mutan Irigwe

Kwamishina Aruwan ya kara da cewa wasu yan bindiga sun sake kai hari kauyen Jankasa dake yankin karamar hukumar Zangon Kataf.

Aruwan yace dakarun sojoji sun samu nasarar dakile harin duk da cewa an harbe wani mutumi mai suna Haruna har lahira.

Hakazalika sojoji sun sake dakile wani harin yan bindiga a yankin Unguwar Rana bayan dogon musayar wuta.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC a jihar Neja

Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, a yankin karamar hukumar Mariga, jihar Neja..

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Bobi ne yayin da ya je gonarsa domin sanya ido ga masu masa aiki ranar Asabar da yamma.

Wata majiya dake kusa da wanda aka sace ya bayyana cewa maharan sun farmaki gonarne a kan mashina shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262