Cuta Ta Barke a Jihar Katsina Ta Hallaka Akalla Mutum 60 Wasu 1,400 Sun Kamu
- Cutar amai da gudawa wacce aka fi sani da kwalara ta hallaka aƙalla mutum 60 a jihar Katsina
- Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Nuhu Danja, shine ya bayyana haka a wurin taron kungiyar likitoci
- Danja yace gwamnati ta ɗauki duk wasu matakai da ya kamata domin magance yaɗuwar cutar
Katsina - Akalla mutun 60 ne suka rasa rayuwarsu a faɗin kauyukan jihar Katsina bayan ɓarkewar cutar kwalara a jihar, Kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Nuhu Danja, shine ya bayyana haka a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar likitoci (NMA).
Sai dai kwamishinan bai bayyana lokacin da suka ɗauki wannan kididdigar rasa rayukan ba, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Wane mataki aka ɗauka bayan ɓarkewar cutar?
Danja ya bayyana cewa a halin yanzun gwamnati na duba dukkan wasu hanyoyin da za'a bi domin dakile yaɗuwar cutar a faɗin kananan hukumomin jihar 34.
Ya kuma kara da cewa gwamnati ta siyo magunguna domin rabawa dukkanin asibitocin dake faɗin jihar.
Kwamishina Danja yace:
"Muna sane da ɓarkewar cutar amai da gudawa a wasu kauyuka jihar mu, gwamnati na iyakar bakin kokarinta wajen dakile cigaba da yaɗuwar cutar."
"Gwamnati ta tanadi dukkan magungunan da zata yaki cutar domin raba su ga dukanin asibitocin jihar."
"A halin yanzun akwai mutum 1,400 da suka kamu da cutar ta amai da gudawa yayin da 60 daga cikinsu suka mutu. Ina amfani da wannan dama wajen kira ga Katsinawa cewa cutar kwalara abun gudu ce."
Tsaftar muhalli da abinci
Kwamshinan lafiya ya kara da gargaɗin Katsinawa da su tabbatar da suna tsaftace mahallin da suke rayuwa a ciki, wanke hannu lokaci bayan lokaci, da wanke kayan itatuwa kafin su ci.
Danja ya gargaɗi masu aikin abinci tun daga mata da sauransu da su tabbatar da suna kulle abincinsu domin magance shigar kwayar cuta.
A wani labarin kuma Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna
Mutum biyar cikinsu harda karamin yaro ɗan shekara 10 suka rasa rayuwarsu yayin harin yan bindiga a yankin karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.
Wannan ya biyo bayan sojoji sun dakile yunkurin wasu yan fashi na sace mutun biyu tare da kuɓutar da wasu shida a wurare daban-daban a karamar hukumar Jema'a.
Asali: Legit.ng