Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a bayan Buhari

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a bayan Buhari

  • Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na mako
  • Ministoci da manyan jami'an gwamnati duk sun hallara a zaman na yau Laraba, 11 ga watan Agusta
  • Zaman na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu ke a birnin Landan inda yake ganin likita

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na tarayya a ranar Laraba, 111 ga watan Agusta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan domin duba lafiyarsa bayan ya halarci babban taron Ilimi na Duniya.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a bayan Buhari
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa Hoto: Independent.ng
Asali: UGC

Kafin fara zaman majalisar, an yi shiru na minti daya don girmama Malami Buwai, tsohon Ministan Noma, wanda ya rasu kwanan nan yana da shekaru 76, jaridar Punch ta ruwaito.

Ministocin da ke halarci taron sun hada da Lai Mohammed, Ministan Yada Labarai da Al'adu; Abubakar Malami, Ministan Shari'a kuma Atoni-Janar na Tarayya.

Kara karanta wannan

Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

Sauran sun hada da Hajiya Zainab Ahmed, Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa; Ministan wutar lantarki, Sale Mamman da Babatunde Fashola, Ministan Ayyuka da Gidaje.

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Ibrahim Gambari, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa, da Babagana Monguno, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa duk sun halarci taron, jaridar The Nation ta ruwaito.

A wani labari na daban, jam’iyyar APC ta dakatar da shugabanta na rikon kwarya na karamar hukumar Yola ta kudu, jihar Adamawa, Alhaji Sulaiman Adamu.

Gidan talabijin na TVC ya kawo rahoto a ranar Talata, 10 ga watan Agusta, 2021, cewa an dauki matakin nan ne saboda zargin Sulaiman Adamu da ake yi da laifi.

Ana tuhumar shugaban jam’iyyar da laifin zagin Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, don haka majalisar gudanar wa a jiha ta kafa kwamitin ladabtar wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel