Yahaya Bello ne matashin dan takarar da zai iya gyara Najeriya, in ji wani sanatan Kogi
- Sanatan jam'iyyar APC daga jihar Kogi ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar da ya fi cancanta ya gaji Buhari
- Ya bayyana cewa, ta fuskar ilimi da gogewa da aiki, to lallai Yahaya Bello ne zai iya zama magajin Buhari mai nagarta
- Sanatan ya dage kan cewa, gwamna Yahaya zai inganta abubuwa da dama suka tabarbare a Najeriya
Sanata Smart Adeyemi (APC – Kogi ta yamma) ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya da ya fi cancanta da gadon shugaba Buhari a zaben 2023, kuma ya daga Najeriya ta fuskar karfin tattalin arzikin duniya.
Sanatan na Kogi ya bayyana gwamnan na Kogi a matsayin gwamna matashi mai dimbin kuzari, da basirar ilimi da sanin makamar aiki tare da tarihi mai kima, ya kara da cewa yana da abin da zai kai kasar nan zuwa tudun na tsira, Daily Sun ta ruwaito.
Da yake rokon ‘yan Najeriya da su yi la’akari da burin zama shugaban kasa na Gwamna Bello, Sanata Adeyemi ya ce idan aka ba shi dama gwamnan zai hada da nasarorin gwamnatin Buhari.
Sanatan yayin da yake amsa tambayoyi jiya daga manema labarai bayan wani shirin karfafawa da ya samar wa mata masu juna biyu 1,000 a mazabarsa, ya bayyana Gwamna Bello a matsayin shugaba mai adalci wanda ke tsoron Allah ya wajen jagoranci.
A cewar sanatan, jihar kafin gwamnatin Bello ta kasance a gurbace da nuna son kai, kabilanci da nadin mukamai; kuma tun lokacin da ya hau karagar mulki ya mayar da adalci da daidaito ya zama abin kallo.
Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta
Yayin da ake tattaunawa game da wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023, masana sun bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar da yafi nagarta, kamar yadda yazo a kuri'ar da jaridar ThisDay ta yi.
Kuri'ar ya biyo bayan hirar da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida yayi da gidan talabijin na Arise TV akan wanda zai zama shugaban Najeriya a 2023.
Osinbajo shi ya cancanci zama shugaban kasa
Baya ga cancantar ilimi, Babangida ya ambaci shekaru da gogewa a matsayin muhimman abubuwan da za su sa a zabi wanda zai maye gurbin Buhari a 2023, inda ya bayyana a sarari cewa ya kamata 'yan Najeriya su zabi mutum mai kuzari wanda bai haura shekaru 60 ba.
Kuri'ar da jaridar ta wallafa a ranar Litinin ta kawo wasu fitattun 'yan Najeriya, tare da Osinbajo cikinsu a matsayin wadanda suka cancanta su rike manyan mukamai a nan gaba.
Sauran wadanda aka kawo sun hada da Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka, Dakta Akinwunmi Adesina da Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed.
Hakazalika da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, da gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, da sauransu.
Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni
A wani labarin, Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yake jagoranta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.
Gwamnonin sun yi wanna jawabin ne a taron da suka gudanar ranar Litinin domin tattauna matsalolin da suka taso a jam'iyyar.
Asali: Legit.ng