Kayataccen bidiyon jami’in dan sandan da ke rawa yayin da yake kula da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja

Kayataccen bidiyon jami’in dan sandan da ke rawa yayin da yake kula da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja

  • An yabawa wani dan sandan Najeriya, Emmanuel Kopwal kan yadda ya saka rawa a cikin aikinsa yayin da yake kula da zirga-zirgan ababen hawa
  • Mutanen da ke bin hanyarsa sun tabbatar da faran-faran din jami’in a duk lokacin da yake bakin aiki, tare da tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa cikin sauki
  • Jami'in Emmanuel wanda ya sami kyaututtuka daban-daban kan aikinsa ya bayyana cewa halayensa kan sa masu ababen hawa kallonsa

Wani dan sandan Najeriya, Emmanuel Kopwal, ya sa mutane suna magana yayin da bidiyon shi yana rawa yayin da yake kula da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja ya bazu a yanar gizo.

Tunde Ednut ya wallafa bidiyon a shafin Instagram, inda aka bayyana jami'in a matsayin mai kula da zirga -zirgar ababen hawa cike da nishaɗantarwa

Kayataccen bidiyon jami’in dan sandan da ke rawa yayin da yake kula da zirga-zirgar ababen hawa a Abuja
Jami'in ya ce masu ababen hawa na son sa Hoto: @daily_trust_news
Asali: Instagram

Maigidansa yana son sa

A cikin hirar da jaridar Daily Trust ta yi da shi, matashin ya ce mutane da yawa da ke bin hanyar da yake karkashin kulawarsa suna yaba masa.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake yunkurin kashe ni sau biyu - Kakakin IBB Afegbua

Dangane da yadda maigidansa ke ɗaukar rawarsa yayin aiki, ya ce sun gaya masa kawai ya kasance mai wayo yayin da yake bakin aiki, ya kara da cewa ba su da matsala da abin da yake yi.

Ya samu lambobin yabo da dama

Ya samu lambobin yabo da yawa Hukumar Burtaniya da ta agaji (reshen Abuja) suna cikin manyan ƙungiyoyin da suka karrama ƙoƙarinsa.

Emmanuel ya bayyana cewa wasu lokutan masu ababen hawa su kan tsaya a gefe don kallo tare da karfafa masa gwiwar ci gaba da abubuwan ban dariyar.

Dangane da hulda da masu ababen hawa da suka saba, ɗan sandan ya ce babu abin da yake yi illa kawai yana yi musu gargaɗi da kada su sake yin tawaye a gaba.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattara wasu daga cikin sharhin a kasa:

jullyjulez ya ce:

"Wannan ba abin ban dariya ba ne ku zo yankin Alausa akwai wanda yake cike da rayuwa kuma yana iya rawa daga safe har dare ko da rana mai zafi."

Kara karanta wannan

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

i_am_renajojo ya ce:

"Wannan da ya yarda da ƙaddararsa ba tare da tambaya ba."

bisithebuilder ya ce:

"Ina son ganin wannan mutumin. Ya sani farin ciki."

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta amince da ware naira biliyan hudu na man motocin aiki na 'yan sanda a fadin jihohi 36 na kasar hadi da Abuja.

An ruwaito cewa, ministan ma’aikatar harakokin 'yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da haka a Abuja a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng