Yanzu-yanzu: 'Yan ta'addan IPOB sun kone fasinja kan karya dokar zaman gida a Imo

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'addan IPOB sun kone fasinja kan karya dokar zaman gida a Imo

  • Mambobin IPOB sun yi wa wani fasinja kurmus a karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo
  • An gano cewa miyagun sun tare motocin dake zuwa Imo daga Umuahia kan dokar zaman gida da suka saka
  • Kafin motar ta kai ga tsayawa, miyagun sun banka mata wuta, lamarin da yasa Nkwogu ya kasa fitowa har ya mutu

Ahiazu Mbaise, Imo - Mambobin IPOB sun kone wani fasinja mai suna Nkwogu a karamar hukumar Ahiazu Mbaise dake jihar Imo sakamakon karya dokar zaman gida na dole da suka saka a ranar Litinin.

Tuni dai dukkannin harkokin kasuwanci suka tsaya a yawancin sassan jihohin kudu yayin da mazauna yankin suke bin dokar da aka saka, Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'addan IPOB sun kone fasinja kan karya dokar zaman gida a Imo
Yanzu-yanzu: 'Yan ta'addan IPOB sun kone fasinja kan karya dokar zaman gida a Imo
Asali: Original

An rufe makarantu yayin da aka hana dalibai masu rubuta jarabawar NECO fitowa domin rubuta jarabawarsu.

Miyagun sun bankawa motar wuta kafin ta tsaya

Daily Trust ta tattaro cewa mamacin yana cikin daya daga cikin motoci bas uku da miyagun suka tsare a titi.

Kara karanta wannan

Yadda masu tattara shara suka dawowa da tsohuwa N10,287,000 da ta zuba a shara

Biyu daga cikin motocin kirar Hummer bas duk mallakin wani kamfanin sufuri ne mai suna Libra wanda suke tahowa daga Umuahia a jihar Abia lokacin da 'yan ta'addan suka tsare matafiyan.

An tattaro cewa miyagun sun harba tayar, lamarin da yasa dole suka tsayar da motar. Fasinjojin dake cikin bas din sun dinga gudun ceton rai inda aka harba daya daga cikin direbobin a kugunsa.

Fasinjan ya kasa fita saboda an bankawa bas din wuta kafin ta tsaya.

Ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da miyagu

Daily Trust ta tattaro cewa an dinga jin harbe-harbe a wurin Banana Junction kan babbar hanyar Orlu zuwa Owerri yayin da 'yan bindiga suka dinga artabu da jami'an tsaro.

Har a yayin rubuta wannan rahoton, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, CSP Mike Abattam bai dauka waya ba yayin da aka dinga kiransa.

'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Kaduna daga 'yan bindiga

A cikin nasarorin da rundunar sojin Najeriya ke samu na kwanakin nan, a halin yanzu sun karba tubabbaun 'yan ta'addan Boko Haram 605 wadanda suka mika makamansu tare da mika wuya ga rundunar, PRNigeria ta tabbatar da hakan.

Ta kara da tattaro cewa an mika tubabbun 229 da suka hada da mata da kananan yara hannun gwamnatin jihar Borno.

A cikin makonnin nan, da yawan mayakan ta'addanci na Boko Haram da iyalansu sun sanar da tubansu kuma sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel