Da duminsa: APC ta aike da sako ga 'yan Najeriya yayin da ‘yan sanda suka karbe hedikwatarta a Abuja

Da duminsa: APC ta aike da sako ga 'yan Najeriya yayin da ‘yan sanda suka karbe hedikwatarta a Abuja

  • A halin yanzu, babu takamaiman bayani kan halin da ake ciki a sakatariyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Abuja
  • A zahirin gaskiya, har yanzu ‘yan jarida a yankin ba su ji daga jam’iyya mai mulki ba kan dalilin da ya sa ‘yan sanda suka kewaye gininta
  • Amma shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai yi wa manema labarai da mazauna yankin bayanin dalilin kasancewar jami'an a wurin

Kasancewar 'yan sanda dauke da makamai a kewayen hedikwatar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Abuja a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ya haifar da tashin hankali da firgici tsakanin mazauna yankin.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, an ga jami'an tsaro masu dauke da makamai a kalla 25 a wurare daban-daban a kan titin Blantyre na yankin Wuse inda sakatariyar jam'iyyar ta kasa take.

Da duminsa: APC ta aike da sako ga 'yan Najeriya yayin da ‘yan sanda suka karbe hedikwatarta a Abuja
Shugabannin APC za su yi jawabi kan dalilin da yasa ‘yan sanda suka karbe hedikwatarsu a Abuja Hoto: APC
Asali: Facebook

Sai dai kuma, domin kwantar da hankulan mutanen da ke cikin rudani, jam'iyyar a takaice ta shaidawa manema labarai cewa nan ba da dadewa ba sakataren yada labaranta na kasa, Sanata John Akpanudoedehe, zai bayyana wa 'yan kasa kudirin 'yan sandan a yankin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasan PDP Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zangar 'Secondus Must Go' a Abuja

Sanarwar ta ce:

"Sakataren jam’iyyar na kasa zai yiwa manema labarai karin haske kan karuwar jami'an tsaro a sakatariyar jam'iyyar ta kasa. Yana kan hanyarsa ta zuwa sakatariyar."

APC za ta fadi zaben Shugaban kasa a 2023: Shahararren malamin addini ya yi hasashe

A wani labari na daban, shahararren malamin addini, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki za ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023.

Ayodele ya fadi haka ne a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, inda ya ce hasashensa zai zama gaskiya idan ba a magance matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ba.

Malamin ya ce 'yan Najeriya sun gaji da jam'iyya mai mulki kuma suna bukatar gyara duk dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta, jaridar PM News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel