'Yan bindiga makare cikin motoci 7 sun kai hari wani sabon ofishin 'yan sanda
- asu tsagerun 'yan bindiga sun afkawa wani sabon ofishin 'yan sanda a jihar Anambra
- Majiya ta bayyama cewa, an yi harbe-harbe tsakanin 'yan bindigan da 'yan sandan ofishin
- An kuma ruwaito cewa, sun tattara wasu makamai da dama daga ofishin na 'yan sanda
Anambra - Wasu 'yan bindiga a cikin motoci bakwai sun afkawa sabon ofishin 'yan sanda na yankin Nnewi inda suka yi awon gaba da makamai.
A cewar wata majiya, 'yan bindigar sun shigo sun yi harbe-harbe na sama da awa daya.
Harbe-harbe tsakanin 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba da 'yan sanda a rundunar 'yan sandan Nnewi a ranar Litinin 9 ga watan Agusta da yamma ya haifar da tashin hankali tsakanin mazauna yankin.
Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun shigo kusan motoci bakwai zuwa ofishin 'yan sanda kuma sun fara harbi wanda ya dauki sama da awa daya.
‘Yan bindiga sun kashe wani bawan Allah, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansar mata da ‘yarsa da suka sace
Wani ganau wanda ba zai so a ambaci sunansa a rubuce ba ya ce 'yan bindigar sun yi nasara kan 'yan sanda inda suka yi awon gaba da makamai.
A cewar majiyar, a lokacin da aka samu karin karfin gwiwa daga rundunar sojojin ruwa, maharan sun tafi duk da an tattara cewa an bi su.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce ofishinsa bai samu wani rahoto kan lamarin ba.
Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane
A wani rahoton, rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani barawon shanu mai shekaru 16, Umaru Muhammed, kan garkuwa da mutane a Ibadan.
Muhammad ya amsa cewa yana cikin gungun masu garkuwa da mutane yayin da yake amsa tambayoyi a hedkwatar rundunar, Eleyele, Ibadan, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa,wanda suka yi awon gaba dashi na karshe sun rude shi da ya zo ya sayi shanu ne a kauyen Akinyele, Karamar Hukumar Akinyele a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Wanda ake zargin da ya amsa cewa shi barawon shanu ne ya ce wasu abokan aikinsa da a yanzu suke nemansa sun ce ya kira mutane su zo su sayi shanu a wurinsa.
Tankar mai ta fadi, ta nike mutane da dama a Ibadan
A wani labarin, Akalla mutane biyar ne wata tankar mai ta murkushe a ranar Litinin a yankin Celica da ke kan sabon hanyar Ife zuwa Ibadan, karamar hukumar Egbeda a jihar Oyo.
Rahoton da Daily Nigerian ta wallafa ya bayyana cewa, tankar mai din ta kubce ne sannan ta kutsa kan wata karamar mota inda ta fada cikin ramin da ke kusa da motar.
Legit Hausa ta tattaro cewa, Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), Kwamandan sashi, Uche Chukwurah, ta tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021.
Misis Chukwurah ta bayyana hatsarin a matsayin mai muni, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar da suka hada da maza uku mata biyu manya.
Asali: Legit.ng