Babban abun da nake tsoro ita ce wutar Jahannama, Shahararren mawakin Najeriya

Babban abun da nake tsoro ita ce wutar Jahannama, Shahararren mawakin Najeriya

  • Fitaccen mawakin nan na zamani, Don Jazzy ya bayyana babban abun da yake tsoro a rayuwarsa
  • Don Jazzy ya ce yana matukar jin tsoron wutar jahannama domin an ce idan mutum ba Kirista bane sai ya shige ta
  • Ya kuma bayyana cewa idan aka duba lamarin kamar ana yi wa mutum barazana ne maimakon a bari ya bi zabinsa

Shahararren mawakin nan na Najeriya wanda aka fi sani da Don Jazzy, ya bayyana babban abin tsoro a rayuwarsa.

Babban mawakin na kungiyar Mavin Records wanda ya yi suna wajen aikin jin kai da taimakon jama’a ya bayyana cewa "wutar jahannama ita ce babbar abin da yake tsoro", jaridar The Nation ta ruwaito.

Babban abun da nake tsoro ita ce wutar Jahannama, Shahararren mawakin Najeriya
Don Jazzy ya ce yana tsoron wutar Jahannama sosai Hoto: Newsbreak.ng
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Don Jazzy ya bayyana wannan lokacin da ya fito a cikin shirin Nancy Isime Show.

Ya ce:

“A halin yanzu, ina tsoron Allah saboda kamar ana yi mana barazana ne da wutar jahannama. Sun ce, idan kai ba Kirista ba ne, za ka shiga wutar jahannama.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan Hausa, Diamond Zahra

“Kamar suna maka barazana ne. Me ya sa ba za ku bar zaɓin a buɗe ba kawai? Me yasa dole ne sai an haɗa shi da wutar jahannama? Bari in yanke shawara.
"Don haka yanzu, dole ne in gaya muku cewa ni Kirista ne saboda ina jin tsoron shiga wutar jahannama. Ina jin tsoro matuka. Wannan shine abin da na sani. Ina jin tsoron wutar jahannama.”

Mun rabu da mahaifiyata lafiya, Mawaki Ala yace yayin da yake zubda hawaye

A wani labari na daban, manyan malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan film, mawaka da sauran daukacin al’ummar musulmi sun yi tururuwa wurin halartar jana’izar mahaifiyar Aminu Ala, shahararren mawakin nan a gidansa dake unguwar Maidile.

Kammala jana’izar ke da wuya aka tattara zuwa kaita makwancinta dake makabartar tarauni. Bayan kammala hakan ne mujallar fim ta tattauna da Ala don jin ta bakinsa inda yace:

"Dukkan rai mamacine kuma yana jiran ranar mutuwarsa don haka ta koma ga mahaliccinta."

Kara karanta wannan

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

Asali: Legit.ng

Online view pixel