Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan Hausa, Diamond Zahra

Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan Hausa, Diamond Zahra

  • Jarumar fina-finan Kannywood Diamond Zahra ta amarce, in ji labari daga na kusa da ita
  • Jarumar da yanzu ta fara tashe ta amarce ne a karshen makon jiya in ji majiyar rahoto
  • An bayyana wani shirin fim da take ciki wanda aka sauya ta saboda yin aure da tayi a yanzu

Kano - Jarumar masana’antar fina-finan Hausa na Kannywood, Zahra Muhammad, wadda aka fi sani da Diamond Zahra ta zama amarya.

Legit Hausa tattaro cewa, jarumar, wadda a yanzu take tashe ta yi aure ne a karshen makon jiya kamar yadda Aminiya ta samu labari.

Jaruma Bilkisu Abdullahi ce ta bayyana hakan a shafinta na Instagram, inda ta sanya hoton Diamond Zahra din sannan ta ce:

“Allah Ya ba da zaman lafiya kawata, Allah Ya albarkaci aurenku.”
Zahra Muhammad | Hoto: aminiya.dailtrust.com
Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan 'Kannywood' Diamond Zahra
Asali: UGC

Jaruma Diamond Zahra ita ce ke jan fim din ‘Gargada’ wanda Ali Nuhu ya dauki nauyi, sannan tana cikin fim din ‘Farin Wata’ na Adam A. Zango.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170

Yanzu haka ana cigaba da daukar shirin na Farin Wata, inda wata majiya ta shaida cewa an musanya jarumar da wata.

Hotunan ango da yayi wuff da zuka-zukan amare 4 a rana daya sun janyo cece-kuce

Wani shahararren dan kasuwa a kasar Gabon ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani bayan ya aura mata hudu a lokaci daya a Libreville.

Dan kasuwan mai suna Mesmine Abessole ya aura mata a wani mashahurin biki da aka yi a ranar Asabar, 31 ga watan Yulin 2021, TheCable ta ruwaito.

Sunayen matan kamar yadda aka tattaro shine Madeleine Nguema, Prisca Nguema, Nicole Mboungou, Carene Sylvana Aboghet, TheCable ta ruwaito.

Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka

A wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo, wasu mata marasa aure a jihar Gombe sun yi kukan neman taimako kan rashin samun mazajen aure.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa mummunan lamarin ya ci gaba tsawon wasu shekaru a yankin arewa maso yammacin kasar, inda ta kara da cewa daruruwan mata marasa aure karkashin jagorancin Suwaiba Isa sun mamaye jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Da aka je aka dawo, BOT ta ceci Shugaban PDP daga yunkurin tsige shi, a nada rikon kwarya

Sun yi hakan ne don zanga-zangar rashin samun mazajen aure ga kimanin su 8,000 a watan Satumban 2018.

Legit.ng ta tattaro cewa sarkin Yarbawa a Gombe, Abdulrahim Alao Yusuf, ya ce kashi 60% na mutanen da ba ‘yan asalin jihar bane sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: