Jami'an kwastam sun murkushe mutum 7 har lahira garin bin 'yan sumoga a Katsina
- Wasu jami'an kwastam da ke aikin sintiri sun hallaka wasu mazauna jihar Katsina bisa kuskure
- Wannan ya faru ne yayin da jami'an ke bin wasu 'yan fasa kwabri a kan titin Jibia na jihar Katsina
- Rundunar ta kwastam a jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce kuma tana kan tattara rahoto
Katsina - Motocin sintiri na hukumar kwastam ta Najeriya sun murkushe mutane bakwai har lahira, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara 13 a kan babbar hanyar Jibia zuwa Kauran.
An tattaro cewa akalla mutane ne 19 suka samu munanan raunuka, in ji rahoton Tribune Nigeria.
Wani mazaunin yankin Abubakar Jibia ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe lokacin da jami’an Kwastam da ke aikin sintirin su ke bin mota kirar J5 Peugeot da ake zargin tana dauke da haramtattun kayayyaki.
Jibia ya shaidawa majiya cewa wadanda abin ya rutsa da su da ake kyautata zaton manoma ne suna tsaye a bakin hanya ne lokacin da motar sintirin ta kauce daga kan babbar hanya ta buge su ta murkushe su nan take.
Ya ce hakan ya jawo hankalin mutanen kauyen inda suka gaggauta zuwa wurin domin ceton rayuka.
Wani shaidan gani da ido, Usman Kabir, ya ce:
“Motar sintiri da motar 'yan fasa kwabri suna gudu kan hanyarsu ta zuwa garin Jibia ne kawai direban motar sintirin ya kauce daga kan hanya ya bi ta kan mutane.
“Mutane shida sun mutu nan take, daya ya mutu yayin da aka garzaya da shi a Babban Asibiti na Amadi Orthopedic Katsina, yayin da sauran 19 da suka samu raunuka yanzu haka suke kwance a asibitin."
'Yan fasa kwabri sun tsere, an kone motar jami'an kwastam
Majiya ta bayyana cewa masu fasa kwabrin sun tsere yayin da fusatattun mutane a wurin da lamarin ya faru suka kona motar jami’an kwastam din kafin isowar jami’an tsaro da suka takaita hargitsin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ta kwastam a jihar Katsina, Danbaba Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce tuni aka fara gudanar da bincike don gano yadda lamarin ya faru, jaridar This Day ta ruwaito.
Ya ce:
“Haka ne, lamarin ya faru. Ya faru ne da jami'an kwastam da ke aikin sintiri na kan iyaka, amma za mu ba ku cikakken bayani saboda muna kan tattara rahoto."
'Yan bindiga makare cikin motoci 7 sun kai hari wani sabon ofishin 'yan sanda
A wani labarin, Wasu 'yan bindiga a cikin motoci bakwai sun afkawa sabon ofishin 'yan sanda na yankin Nnewi inda suka yi awon gaba da makamai. A cewar wata majiya, 'yan bindigar sun shigo sun yi harbe-harbe na sama da awa daya.
Harbe-harbe tsakanin 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba da 'yan sanda a rundunar 'yan sandan Nnewi a ranar Litinin 9 ga watan Agusta da yamma ya haifar da tashin hankali tsakanin mazauna yankin.
Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun shigo kusan motoci bakwai zuwa ofishin 'yan sanda kuma sun fara harbi wanda ya dauki sama da awa daya.
Asali: Legit.ng