Karin Bayani: Yadda Motar Kwastam Ta Kwace Ta Yi Kan Jama'a Ta Hallaka Mutum 15 a Katsina

Karin Bayani: Yadda Motar Kwastam Ta Kwace Ta Yi Kan Jama'a Ta Hallaka Mutum 15 a Katsina

  • Wata motar kwastam ta kucce ta yi kan jama'a yayin da ta biyo yan fasa kwauri a garin Jibia dake jihar Katsina
  • Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin da ya afku ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 15 tare da jikkata wasu da dama
  • Mazauna garin sun fito zanga-zanga don nuna fushinsu kan abinda ya faru, matasa sun kone motar kwastam

Jibia, Katsina - Mutane sun fito zanga-zanga a garin Jibia, jihar Katsina, kan kashe wasu mutum 15 da jami'an kwastam suka yi yayin da suka biyo masu fasakwaurin shinkafa.

Wasu shaidu sun bayyana cewa mutane da dama sun samu jikkata kuma a halin yanzun suna gadon asibiti ana kulawa da lafiyarsu.

Shaidun sun tabbatar da cewa wata motar jami'an kwastam ce ta yi kan dandazon mutane yayin da suka biyo wasu da ake zargin yan fasa kwaurin shinkafa ne a yankin.

Motar jami'an kwastam ta hallaka mutum 5 a Katsina
Da Dumi-Dumi: Mutum 5 Sun Mutu Yayin da Kwastam Suka Biyo Yan Fasakwaurin Shinkafa a Katsina
Asali: UGC

Rahotan jaridar Aminiya ya nuna cewa a sakamakon haka mutum 10 sun mutu nan take, yayin da karin wasu biyar suka biyo baya.

Me ya jawo hatsarin?

Wata majiya da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Premium times cewa:

"Sun biyo yan fasa kwauri cikin matsanancin gudu, direban ya kasa sarrafa motar ta yi cikin jama'a inda ta hallaka mutane da dama. Wannan shine dalilin zanga-zanga."
"Fusatattun matasa dake cikin masu zanga-zangar sun yi kaca-kaca da motar jami'an kwastam din."

Me hukumomi suka ce game da lamarin?

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce, ya zuwa yanzun ba shi da rahoto a kan lamarin, amma yana jiran rahoton DPO na ’yan sandan Jibia.

Hakazalika, har zuwa yanzun hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) ba tace komai ba game da lamarin da ya faru.

A wani labarin kuma Fusatattun Matasan PDP Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zangar 'Secondus Must Go' a Abuja

Fusatattun matasan jam'iyyar PDP sun mamaye wasu titunan Abuja suna neman a sauke shugaban PDP, Uche Secondus, cikin gaggawa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Matasan karkashin kungiyar ceto PDP daga rushewa, waɗanda daga baya suka tattarru a sakareriyar PDP ta kasa, sun ɗauki wannan matakin ne saboda ficewar wasu gwamnoni zuwa APC a baya bayannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel