Babbar Magana: A Karon Farko, Babban Limamin Makka Sheikh Sudais Ya Naɗa Mata Mataimakansa

Babbar Magana: A Karon Farko, Babban Limamin Makka Sheikh Sudais Ya Naɗa Mata Mataimakansa

  • Shugaban hukumar kula da masallai masu tsarki na Makka da Madina, Sheikh Sudais ya naɗa mata mataimakansa
  • Wannan ne dai karon farko da mace zata rike babban mukami a hukumar kula da masallatai
  • Hakanan hukumar ta sanar da cewa zata fara baiwa mata horo don haɓɓaka ayyukan matan a masallatan biyu

Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta bayyana naɗa mata a manyan mukamai na hukumar dake kula da masallatai biyu mafiya daraja dake Makka da Madina.

A ranar Litinin ɗinnan ne kafar watsa labarai ta Al-Arabiyya tv, wadda mallakin Kasar Saudiyya ne, ta bada rahoto kan cigaban.

Rahoton BBC Hausa ya bayyana cewa Shugaban hukumar, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya naɗa mata guda biyu a matsayin mataimakansa.

Sheikh Abdulrahman Al-Sudais
Babbar Magana: A Karon Farko, Babban Limamin Makka Sheikh Sudais Ya Naɗa Mata Mataimakansa Hoto: saudi24news.com
Asali: UGC

Matan da shugaban hukumar ya naɗa sun haɗa da Dakta Al-Anoud Al-Aboud da kuma Dakta Fatima Al-Rashoud.

Za'a baiwa mata horo mai taken 'Hayyak'

Rahoton Al-Arabiyya ya kara cewa hukumar kula da masallatan biyu zata horad da mata ma'aikata 320 yan asalin Saudiyya.

Hukumar ta bayyana cewa horon mai taken 'Hayyak' zai taimaka wajen haɓɓaka ayyukan mata a masallatai biyu mafiya daraja, kamar yadda BBC ta ruwaito.

A baya ma'aikatar shari'a ta naɗa mata 100

Wannan ba shine karon farko ba, inda a shekarar da ta gabata ma'aikatar shari'a ta kasar Saudiyya ta sanar da naɗa mata 100 a ɓangarori da dama na shari'a.

Jagoran sabbin waɗanda aka naɗa a mukaman, Dr Hala al-Tuwaijri, tace:

"Gwamnatin Saudiyya ta saka taimakon mata a gaba, inda take ɗorawa a kan tsare-tsarenta na baya."

Yariman Saudiyya mai jiran gado, Muhammad Bin Salman, shine ya kirkiro da wani kudiri mai taken Muradin 2030, wanda zai baiwa mata damar fitowa a dama dasu a kowane bangaren gwamnati.

A wani labarin kuma Gwamna Zulum Ya Bayyana Yadda Yake Farin Ciki da Yan Boko Haram/ISWAP Suke Tuba a Borno

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana jin daɗinta yayin da ake kara samun karuwar yan ta'adda suna tuba su mika makamansu ga sojoji a jihar, Kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Borno, Alhaji Babakura Abba-Jato, shine ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron tsaro a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel