Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasan PDP Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zangar 'Secondus Must Go' a Abuja

Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasan PDP Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zangar 'Secondus Must Go' a Abuja

  • Wasu matasa yan jam'iyyar PDP sun fito zanga-zangar neman a sauke shugaban PDP, Uche Secondus
  • Matasan karkashin kungiyarsu mai fafutukar ceto PDP daga rushewa sun bayyana cewa shugaban ya gaza
  • A cewar shugaban masu zanga-zangar Secondus yana da wata manufa da yake son cimmawa a PDP

FCT Abuja - Fusatattun matasan jam'iyyar PDP sun mamaye wasu titunan Abuja suna neman a sauke shugaban PDP, Uche Secondus, cikin gaggawa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Matasan karkashin kungiyar ceto PDP daga rushewa, waɗanda daga baya suka tattarru a sakareriyar PDP ta kasa, sun ɗauki wannan matakin ne saboda ficewar wasu gwamnoni zuwa APC a baya bayannan.

Matasan suna rike da kati wanda aka rubuta "Secondus Must Go" wato wajibi Secondus ya sauka, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Wasu kuma na rike da "Mun gaji da jagorancin ka" "Ba zamu jure cigaba da rasa gwamnoni ba" da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Yar Takarar Sanata a APC Ta Jagoranci Yan Jam'iyya Akalla Mutum 80,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Matasan PDP sun fito zanga-zanga a Abuja
Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasan PDP Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zangar 'Secondus Must Go' a Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Menene ainihin makasudin zanga-zangar?

Da yake zantawa da manema labarai a sakateriyar PDP, shugaban masu zanga-zangar, Com. Tamunotonye Inioribo, ya bayyana cewa idan Secundus ya sauka daga mukaminsa PDP zata samu hanyar saisaita kanta gabanin zaɓen 2023.

A jawabinsa, yace:

"Muna zarginsa da sanya son rai a cikin jam'iyyar PDP, kuma duk laifinsa ne yasa gwamnoni uku tare da sanatoci da yawa suka fice zuwa APC."
"Manyan ginshikan jam'iyya da suka haɗa da gwamnonin PDP, kwamitin guadanarwa da kwamitin zartarwa duk ya raba kawunan su."

Tamunotonye ya kuma zargi shugaban da rarraba jam'iyyar PDP a jihohi sabida son ransa da kuma wani kudiri da yakeson cimma wa.

Wane mataki PDP ta ɗauka don magance rikici?

Bayan wannan cece-kuce da ake ta samu a PDP, Kwamitin amintattu na jam'iyyar ya kira taro da zummar nemo hanyar warware matsalolin da suka taso.

Da kuma matsalolin da wasu ƙusoshin jam'iyyar bakwai suka gabatar yayin da suka yi murabus daga muƙamansu a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya yi muni yayin da aka nemi shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ya yi murabus

Duk da cewa mambobin BoT sun cimma matsaya inda suka kafa kwamitin sansantawa, amma maganar tunbuke Secondus ba ta bi ruwa ba.

Matasa sun fito zanga-zanga a Abuja
Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasan PDP Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zangar 'Secondus Must Go' a Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yanzun haka gwamnoni PDP suna gudanar da taro

A halin da ake ciki yanzun gwamnonin dake karkashin jam'iyyar PDP sun shiga taron sirri a gidan gwamnan jihar Akwa Ibom dake Asokoro da zummar gano hanyar warware wannan dambarwa.

Taron yana gudana ne karkashin jagorancin gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shugaban gwamnonin PDP.

A wani labarin kuma Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya

An gano gawar wani ango a ƙasar Habasha kwanakin kaɗan bayan ɗaura masa aure a garin Nekemte dake yammacin Habasha, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzun an damke mutum 6 da ake zargin suna da hannu a kisan angon ciki harda amaryarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel