Babbar Jigon APC Ta Kasa Ta Jagoranci Mutum 80,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP
- Yar takarar sanata karkashin APC a zaɓen 2019 ta jagoranci magoya bayanta sun canza sheka zuwa APC a jihar Benuwai
- Adzape-Orubibi, ta bayyana cewa dalilinta na ficewa daga APC shine jam'iyyar ta gaza ta kowane fanni
- Gwamna Ortom ya jaddada cewa PDP a shirye take ta tarbi duk wanda ke son dawo wa cikinta
Benue - Yar takarar sanatan Benuwai ta kudu-gabas ƙarkashin jam'iyyar APC a zaɓen 2019, Mimi Adzape-Orubibi, ta sauya sheka zuwa PDP tare da magoya baya 80,000 ranar Asabar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Taron tarbar masu sauya shekar, wanda ya gudana a garin Adikpo, hedkwatar karamar hukumar Kwande sai da ya tsayar da hada-hada a mazabar sanata ta kudu-gabas jihar Benuwai.
Yayin jawabinta ga ɗumbin mahalarta taron, Adzape-Orubibi, tace babban dalilinta na ficewa daga APC shine saboda gazawar jam'iyyar wajen magance matsalar tsaro da tattalin arziki.
A jawabinta tace:
"Rashin tsaro a mulkin APC ya kai matakin da ya gurguntar da ɓangaren samar da abinci a jihar Benuwai saboda sama da mutum miliyan ɗaya sun zama yan gudun hijira a faɗin jihar."
"Tattalin arzikin Najeriya ya yi muni sosai. Yan Najeriya na rayuwa cikin matsanancin talauci saboda tashin frashin kayan masarufi, ba zamu cigaba a haka ba."
"Saboda haka na yanke shawarar komawa PDP tare magoya bayana 80,000 kuma akwai waɗanda zasu biyo baya nan gaba."
Shin jam'iiyyar PDP ta shirya kuwa?
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, yace saboda gazawar APC, jam'iyyar PDP a shirye take ta tarbi duk maison shigowa cikinta.
Gwamnan ya jaddada cewa PDP zata lallasa APC ta kwace mulki a 2023 saboda kasawar jam'iyyar a kowane ɓangare.
A jawabinsa, gwamna Ortom yace:
"Mutanen Benuwai basu da sauran alfarmar da zasu wa APC domin ta gaza aiwatar musu da alkawuranta. Duk wani fatan mutanen Benuwai ya dogara ne a kan PDP."
"PDP tana da kwarewar da zata saisaita komai ya koma kamar da ba wai kamar yadda APC ta yi na lalata ƙasa ba, wannan shine abinda APC ta yi a ƙasar mu."
A wani labarin da muka kawo muku na daban kuma tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, IBB, ya bayyana babban dalilin da yasa sama da shekara 10 bai aure ba.
IBB yace a wancan lokacin bai sha wahala ba wajen samun matar da zai aura amma yanzun abun ba shi da sauki, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Allah ya yiwa matar Janar Ibrahim Badamasi Babangida rasuwa tun a shekarar 2009 kuma har zuwa yanzun bai sake wani auren ba.
Asali: Legit.ng