Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya
- An cafke wata amarya da wasu mutum 5 a kasar Habasha da zargin kashe angonta kwanaki kaɗan bayan aurensu
- Da farko angon ya bata, amma binciken yan sanda ya gano gawarsa a bakin tafkin wajen gari
- Yar uwarsa ta bayyana cewa an kammala aurensa cikin jin dadi amma sai wannan lamarin ya faru
Ethiopia - An gano gawar wani ango a ƙasar Habasha kwanakin kaɗan bayan ɗaura masa aure a garin Nekemte dake yammacin Habasha, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Angon mai suna Gemechis Mosisa, ma'aikacin jinyane ɗan kimanin shekara 28, ya wallafa sakon aurensa a dandalin sada zumunta na facebook ranar Asabar.
Bayan kwana ɗaya, wato ranar Lahadi Mosisa ya sanya hotunan shagalin bikin a dandalin.
Shin amarya na da hannu a kisan?
Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzun an damke mutum 6 da ake zargin suna da hannu a kisan angon ciki harda amaryarsa.
Wata yar uwarsa, Chala Inkosa tace:
"A cikin coci aka daura wa Gemechis aure kuma bikin auren gwanin ban sha'awa. Iyalinsa na cikin bakin ciki bayan da murnarsu ta koma abin takaici''.
Iyalan angon sun bayyana cewa ya fita gida ranar Lahadi da ta gabata, kuma kowa ya yi tsammanin zai samu halartar liyafar da aka shirya a gidan surukansa amma bai zo ba.
Bayan bacewarsa, wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Yayin da makusanta yan uwa da abokan arziki suka sanar da bacewar angom, jami'an yan sandan Habasha suka fara bincike kan lamarin.
BBC hausa ta rahoto cewa kwana biyu da fara bincikensu ne suka gano gawarsa a cikin wani karamin tafki dake kusa da garin.
Shugaban masu bincike a garin Nekemte, Misganu Wakgari, yace:
"An gano kwat dinsa rataye akan bishiyar da ke kusa. An kuma gano zobensa na zinari da agogonsa. A halin yanzun muna cigaba da bincike."
A wani labarin da muka kawo muku na daban kuma tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, IBB, ya bayyana babban dalilin da yasa sama da shekara 10 bai aure ba.
IBB yace a wancan lokacin bai sha wahala ba wajen samun matar da zai aura amma yanzun abun ba shi da sauki, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Allah ya yiwa matar Janar Ibrahim Badamasi Babangida rasuwa tun a shekarar 2009 kuma har zuwa yanzun bai sake wani auren ba.
Asali: Legit.ng