Ku shiga siyasa idan kuna son Najeriya ta samu ci gaba, Gwamna ya bukaci Malaman addini
- Siyasa a kowane mataki ba na shugabanni da ‘yan siyasar da ke gwamnati bane kawai; 'yan kasa suna da rawar ganin da za su taka
- Wannan shine ra'ayin Gwamna Seyi Makinde lokacin da yayi magana a cocin Christ Revival Miracle Church a Ibadan a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta
- Gwamnan na Oyo ya ce hanya daya da 'yan kasa za su samu irin shugabancin da suke so shi ne su shiga siyasa
Ibadan, Oyo - Ga gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, harkar siyasa ta dukkanin masu sha'awar ci gaban ƙasa da bunkasar ƙasar ne.
Wannan shine dalilin da ya sa gwamnan a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, ya ƙarfafa wa malaman cocin Christ Revival Miracle Church, Ibadan, gwiwar cewa su shiga siyasa.

Asali: Facebook
Gwamna Makinde ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya halarci wani taron cocin wanda babban jagoransa, Reverend Peter Folorunso Owa ya shirya.
A cikin jawabinsa, Makinde ya bayyana cewa ta hanyar shiga cikin ayyukan siyasa ne 'yan ƙasa za su iya samun jerin shugabannin da za su taimaka musu wajen cimma burinsu na gama gari.
Ya ce:
"Na kuma karfafa wa duk wanda ke a nan gwiwar cewa ya shiga siyasa da shugabanci, saboda ta hanyar shigar mu ne jihar mu da kasar mu za su samu irin shugabancin da suke so."
A wani labari na daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da ya daina jaje kan hauhawar hare-haren 'yan bindiga a jiharsa.
A yayin karbar bakuncin Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa wanda ya kai ziyara jihar Katsina a ranar Alhamis, Masari ya ce goma daga cikin kananan hukumomin jihar na fuskantar harin 'yan bindiga a kullum.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce rashin tsaron da jihar Katsina ke fuskanta na hana shi bacci.
Asali: Legit.ng