PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa

PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa

  • Jam'iyyar PDP ta yi kira ga Gwamna Aminu Masari da ya fito fili ya sanar da Buhari cewa ya gaza
  • Sakataren yada labarai na babbar jam'iyyar hamayyar yace abun kunya ne yadda 'yan bindiga suka kwace Katsina
  • Kola yace shugaban kasa Buhari ya gaza domin dukkan alkawuransa na tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa sun kasa cika

Katsina - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da ya daina jaje kan hauhawar hare-haren 'yan bindiga a jiharsa, TheCable ta wallafa.

A yayin karbar bakuncin Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa wanda ya kai ziyara jihar Katsina a ranar Alhamis, Masari ya ce goma daga cikin kananan hukumomin jihar na fuskantar harin 'yan bindiga a kullum.

PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa
PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce rashin tsaron da jihar Katsina ke fuskanta na hana shi bacci.

PDP ta caccaki Masari da shugaban kasa Buhari

Kara karanta wannan

Tsufa na damun shi: Don ya bayar da dalilai 4 da suka sa IBB ya caccaki Buhari, Atiku da Tinubu

A yayin martani ga zancensa, a ranar Lahadi, Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP na kasa, yace ya dace Masari ya fito fili ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC cewa gwamnatin tarayya ta gaza.

Masari baya yi wa jama'arsa da suka fada tuggun 'yan bindiga adalci. Ganin yadda cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza kuma ya kasa tsare kasar nan. Ya saka siyasa a ransa ta yadda ya kasa sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari gazawarsa.
Tabbas abun takaici ne da gazawa irin ta shugaban kasa Muhammadu Buhari da za a ce 'yan bindiga sun kwace kasarsa. Sun kwace kananan hukumomi ta yadda suke kashe-kashe, fyade da halaka jama'a.
Shugaban kasa ya sha alwashin yakar ta'addanci amma yayi biris da kiran mutane yana cigaba da morewa a Aso Rock, Abuja.
Abu ne sananne cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza. Alkawurransa na tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa a bayyane suke ba zasu cika ba.

Kara karanta wannan

Kullum sai an kai hari kananan hukumomin Katsina 10, Aminu Bello Masari

Obasanjo ya lallaba Kwatano domin nemawa Igboho mafaka da afuwa

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasabjo ya kai ziyara jamhuriyar Benin a makon farko na Augustan 2021 kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Manyan majiyoyi sun sanar da theCable cewa sai da tsohon shugaban kasar ya biya ta tsibirin Zanzibar dake Tanzania a ranar 1 ga watan Augusta kafin ya wuce Benin din.

Ya kai ziyarar ne don yin ta'aziyya ga Nicephore Soglo wanda bai dade da rasa matarsa Roseline Soglo ba. Roseline ta rasu ne a ranar 25 ga watan Yuli tana da shekaru 87 a Cotonou.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng