Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar

Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar

  • An nemi shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, da ya gaggauta yin murabus
  • Masu ruwa da tsaki a majalisar wakilai ne suka yi wannan kira kwanan nan a cikin wata sanarwa bayan wani taron yanar gizo
  • Har ila yau, 'yan majalisar sun ce shugaban ya kasa tafiya da mambobin jam’iyyar kuma cewa zai lalata jam'iyyar idan aka ba shi damar ci gaba

Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun nemi shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus, da yayi murabus daga mukaminsa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mambobin kungiyar masu ruwa da tsakin, a cikin wata sanarwar da shugabanta, Kingsley Chinda (PDP, Ribas) da Mataimakinsa, Chukwuka Onyema (PDP, Enugu) suka sa hannu, sun yi wannan kiran ne bayan wata ganawa da suka yi a ranar Asabar.

Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar
Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar Hoto: Prince Uche Secondus
Asali: Facebook

Sun dora alhakin matsalolin da ke faruwa a jam'iyyar a kan "halayar jagoranci" na Mista Secondus.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

'Yan majalisar na PDP sun kuma zargi Mista Secondus da rashin tafiya tare da 'yan jam'iyyar, inda suka kara da cewa idan aka ba shi damar ci gaba da mulki a cikin watanni uku masu zuwa, jam'iyyar za ta shiga cikin hadari.

Sun nemi Kwamitin Amintattu (BOT) na jam'iyyar da kungiyar Gwamnonin PDP da su fara sake fasalin jam'iyyar, The News ta ruwaito.

Wa'adin Mista Secondus da sauran membobin Kwamitin Aiki na jam’iyyar na Kasa (NWC) zai kare a watan Disamba bayan an zabe shi a wa'adin shekaru hudu a watan Disamba 2018.

Rikicin PDP ya yi muni yayin da aka nemi shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ya yi murabus

A baya mun kawo cewa, rikicin da ke girgiza Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ci gaba da ƙaruwa duba da buƙatar da ƙungiyar PDP a Arewa ta gabatar na murabus ɗin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Uche Secondus.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP

Kungiyar ta arewa wadda ta yi ikirarin wakiltar muradun 'yan siyasa daga jihohin arewa 19 da Abuja, ta bukaci Secondus da ya sauka daga kujerarsa domin ceto jam'iyyar daga durkushewa baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel