Ke duniya: Yaro mai shekara 9 yayi garkuwa da dan makwabta mai shekara 4 a Kano

Ke duniya: Yaro mai shekara 9 yayi garkuwa da dan makwabta mai shekara 4 a Kano

  • Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da sace yaro mai shekaru 4 da dan makwabcinsu mai shekaru 9 yayi
  • Kamar yadda iyayen yaron suka sanar, sun ga dan makwabcinsu Abubakar ya goya dan su, amma basu sake ganinsa ba
  • Bayan tsananta bincike, Hisbah ta gano cewa Abubakar ya jefa Musa a wani rami dake Kofar Dawanau

Dala, Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta tabbatar da sace wani yaro mai shekaru hudu mai suna Musa wanda wani yaron makwabcinsu mai suna Abubakar mai shekaru 9 yayi a Dandishe dake karamar hukumar Dala ta jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a yayin bada labarin yadda lamarin ya faru a ranar Asabar, mai magana da yawun Hisbah, Lawan Fagge, ya ce batan Musa yasa iyayensa suka kai kara hukumar Hisbah dake Dala.

Ke duniya: Yaro mai shekara 9 yayi garkuwa da dan makwabta mai shekara 4 a Kano
Ke duniya: Yaro mai shekara 9 yayi garkuwa da dan makwabta mai shekara 4 a Kano. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Da wa aka ga Musa na karshe a ranar da ya bata?

Iyayen Musa kamar yadda ya sanar, sun ce a ganinsa na karshe da aka yi, an gan shi a bayan Abubakar kuma har yanzu ana ta nemansu amma ba a gansu ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Benin Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Baiwa Sunday Igboho Mafaka

Fagge ya ce an kama Abubakar da iyayensa lokacin da aka fara bincike domin gano yadda aka yi yaron ya bace, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hisbah ta fara tuhumar wanda ake zargi

A yayin tuhuma, Abubakar yayi ikirarin cewa wani mutum ya bukaci ya sato Musa kuma da ya dauke shi ya mika masa.

A yayin da aka tambaya Abubakar ko zai gane mutumin, ya amsa da eh kuma ya jagoranci Hisbah har zuwa wani gareji da ke Kofar Ruwa kuma yace shugaban ne yasa shi ya dauko yaron.
Yayin da Hisbah ta fara tuhumar mutumin mai suna Malam Uba Tofa, wanda tsohon soja ne, yace bai san komai game da abinda ake tuhumarsa ba kuma bai taba ganin Abubakar ba a rayuwarsa.
Daga nan jami'an Hisbah sun gano cewa karya Abubakar yake kuma ya kasa fadin inda mutumin yake har na tsawon kwanaki hudu," Fagge yace.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

Abubakar ya bayyana gaskiyar lamari

A rana ta biyar ana cigaba da bincike, Abubakar yace ya sace Musa kuma ya wurga shi wani rami dake Kofar Dawanau. Ya jagoranci Hisbah amma kuma ba a ga Musa ba.

Sai dai bayan bincike ya tsananta, an samu Musa cikin koshin lafiya a gidan dagacin Kofar Dawanau.

Hisbah ta sha alwashin yin adalci

A bangaren darakta janar na Hisbah, Aliyu Kibiya, yayi kira ga jama'ar Dandishe da su kwantar da hankalinsu domin za a yi adalci ga yaron da aka sace kuma sai an kakkabe dukkan bata-gari a yankin da kewaye.

A yayin jawabi, mahaifin Abubakar, Malam Abdullahi, ya jinjinawa jami'an Hisbah kan jajircewarsu na ceton yaron inda ya sha alwashin zai kasance mai saka ido a nan gaba.

A bangarensa, Malam Babangida, mahaifin Musa, ya mika godiyarsa ga Allah da ya sada shi da dansa cike da koshin lafiya.

Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa

Chris Ngige, ministan kwadago na Najeriya yace ya ja kunnen 'ya'yansa likitoci da kada su kuskura su shiga wannan yajin aikin da ake yi wanda ya kwatanta da "rashin hankali".

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta shiga yajin aiki saboda zargin gwamnatin tarayya da take da karya yarjejeniyar da suka yi da kungiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kokarin da gwamnatin take yi na ganin cewa likitocin sun janye yajin aikin da suka fada ya gagara.

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel