Rigimar cikin gidan PDP ta kara cabewa, wasu jerin shugabanni na barazanar murabus kwanan nan

Rigimar cikin gidan PDP ta kara cabewa, wasu jerin shugabanni na barazanar murabus kwanan nan

  • Wasu ‘yan majalisar NWC na barazanar barin mukamansu a Jam’iyyar PDP
  • Shugaban matasan PDP na kasa, Okoye, ya na cikin wadanda suka huro wuta
  • PDP ta na fuskantar rikicin cikin gida a karkashin jagorancin Uche Secondus

Abuja – The Cable ta ce wasu mutum hudu daga cikin ‘yan majalisar aiwatar wa watau NWC na jam’iyyar adawa ta PDP, suna barazanar sauka daga kujerunsu.

Rahoton ya bayyana cewa wadannan shugabanni hudu suna barazanar yin murabus idan jam’iyyar ta gagara kawo karshen rikicin da ake ta fama da shi.

Udeh Okoye ya bada wa'adin kwanaki hudu

Daga cikin masu wannan ra’ayi akwai shugaban matasa na jam’iyyar PDP na kasa, Udeh Okoye.

The Nation ta ce Okoye ya ja-kunnen PDP cewa wasu shugabanni za su iya barin jam’iyyar saboda irin rikon Uche Secondus, wanda ya ce ya gaza kawo masu gyara.

“Na fada masa (Uche Secondus) a wajen taronmu na majalisar NWC cewa ya sauka daga kujerarsa domin ba zai iya jagorantar jam’iyyar nan zuwa ga nasara ba.”

Kara karanta wannan

Yunkurin korar Secondus da sauran Shugabannin PDP ya sa Gwamnoni sun rabu zuwa gida uku

“Ina kuma kira ga shugabanni, gwamnoni, matasa, mata da iyayen PDP su cece ta daga Secondus. Idan ba ayi haka ba, zan yi murabus nan da kwana hudu.”

Rigimar cikin gidan PDP
Taron PDP a Ondo Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Zunuban Prince Uche Secondus a PDP

Silar rigimar da ake yi a jam’iyyar hamayyar ita ce wasu gungu ba su tare da Prince Uche Secondus, wanda ke neman ya zarce a kujerarsa a zaben Disamba.

Daga cikin manyan zargin da ake yi wa shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus, akwai rashin gaskiya da rike amana wajen kula da baitul malin jam’iyya.

Shugabannin PDP da suka yi murabus a cikin makon nan sun karfafa wannan zargi, bayan cewa ba a tafiya da su, suna zargin Uche Secondus da cin kudin jam’iyya.

Kassim Afegbua ya na cikin masu jifar Uche Secondus da wannan zargi. A dalilin haka shugaban na PDP ya kai karar Afegbua a kotu, da cewa ya na bata masa suna.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: PDP ta saki bidiyo, ta yanke muhimmiyar shawara

Ana ficewa daga Jam'iyya, a shiga APC

A karkashin jagorancin Prince Uche Secondus, jam’iyyar PDP ta rasa gwamnoni uku zuwa APC.

Gwamnonin da suka bar jam’iyyar PDP, suka koma APC mai mulki sune; David Umahi (Ebonyi); Ben Ayade (Kuros Riba), da Muhammad Bello Matawalle (Zamfara).

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel