2023: IBB ya bayyana abubuwa guda 8 da suka zama dole wanda zai gaji Buhari ya kasance da su
Ana iya cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), tsohon shugaban kasar Najeriya, yana da karfi idan aka zo batun siyasa a kasar.
Yayin yakin wanda zai gaji shugaba Muhamadu Buhari bayan karewar wa'adin mulkinsa a 2023 ke kara karfi a tsakanin mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP), kalaman dan siyasan na iya kawo cikas ga wasu.
A wata hira ta musamman da Arise TV a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, tsohon shugaban mulkin sojin ya gargadi ‘yan Najeriya akan zabar wani tsohon dan siyasa don ya gaji shugaba Buhari a babban zabe mai zuwa.
Sai dai, ya ba da shawara da a zabi matashi kuma mai kuzari wanda bai wuce shekaru 60 da haihuwa ba don zama shugaban ƙasa na gaba.
A nan Legit.ng ta gabatar da halayen da IBB ya ce ya zama dole matashin ɗan siyasar da ke son ya gaji Buhari a 2023 ya mallaka:
1. Dole ne kada dan takarar shugaban kasa ya haura shekara sittin
2. Dole ne ya fahimci manyan matsalolin kasar
3. Dole ne dan takarar da ya dace ya zama jagoran Najeriya nagari
4. Dole ne ya kasance mutum da ya yi tafiya sosai a duk fadin Najeriya
5. Dole ne ya kasance yana da abokai a ko'ina
7. Dole ne ya kasance ɗan siyasa nagari
8. Ya kamata ya iya yin magana da 'yan Najeriya
IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba
A gefe guda, tsohon shugaban kasan mulki soja, Ibrahim Babangida ya kara yin magana kan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 inda yace babu shakka mummunan juyin mulki za a tafka a kasar nan da ba a soke shi ba.
Zaben an yi shi ne tsakanin Bashir Tofa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) da MKO Abiola na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari
Duk da Abiola ne ya ci zaben kamar yadda sakamako ya nuna, an soke zaben tun kafin jami'ai su bada sanarwan wanda yayi nasara.
Asali: Legit.ng