An garkame masu addinin gargajiya a kurkuku kan kai wa Musulmai hari a Masallaci

An garkame masu addinin gargajiya a kurkuku kan kai wa Musulmai hari a Masallaci

  • Wasu masu addinin gargajiya na tsare a gidan yari bayan sun kai wa Musulmi hari a masallaci a jihar Ogun
  • An bayar da umurnin tsare su ne a yayin sauraron shari’ar wata arangama tsakanin bagarorin biyu a lokacin bikin masu addinin gargajiya na Oro
  • A lokacin bikin na Oro, masu addinin gargarjiya sun hana fita a yankin, wanda hakan ya gurgunta harkoki

Jihar Ogun - Wata kotun majistare da ke zaune a Ota, karamar hukumar Ado Odo Ota a jihar Ogun ta daure wasu masu addinin gargajiya su biyar a cibiyar gyaran hali saboda zarginsu da kai wa wasu Musulmi hari a yankin Idiroko na jihar.

Masu addinin gargajiyan da Musulmai sun yi artabu kan bikin Oro na shekara-shekara a Idiroko da ke karamar hukumar Ipokia ta jihar.

An garkame masu addinin gargajiya a kurkuku kan kai wa Musulmai hari a Masallaci
Masu addinin gargajiyan da Musulmai sun yi artabu kan bikin Oro Hoto: Thisday
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mabiya Oro sun sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin, don shirye-shiryen bikin Oro na bana, amma ci gaban ya haifar da rikici a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan addinin gargajiya da Musulmai a Ogun, Malamin addini ya jigata

An bayar da rahoton cewa tashin hankali ya barke lokacin da masu addinin gargajiyan suka kai hari kan musulmai da ke sallar magariba.

Sai dai a jiya ‘yan sanda sun gurfanar da mutane biyar da ake zargi a gaban alkali A. O. Adeyemi a Ota.

Aminiya ta ruwaito cewa kotun ta bayar da belin masu addinin gargajiyar, amma sun kasa cika sharuddan belin.

Alkalin kotun, ya bayar da umurnin a ci gaba da tsare su a cibiyar gyara hali na Ilaro, har sai sun cika sharuddan. Adeyemi ya daga sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Agusta.

Mai magana da yawun ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci yankin domin fadakar da jama’a kan dalilin da ya sa baya bisa doka sanya dokar hana fita da rana a karni na 21.

Kakakin ya yi mamakin dalilin da ya sa wasu mutane za su hana Musulmi da Kirista bauta wa Allahansu, da sunan bikin Oro.

Kara karanta wannan

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

Kotu ta daure wani dodo da ya kai hari ofishin 'yan sandan Najeriya

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke zaman ta a Makurdi, babban birnin jihar Benuwe, ta tura wasu mutane 10 gidan yari bayan samun su da laifin kai hari ofishin 'yan sandan Najeriya da ke karamar hukumar Ado.

Kotu ta bukaci a ajiye mutanen a gidan yari har sai ta saurari shawarar masana shari'a. Mutanen su ne; Emmanuel Obande, Daniel Ogbu, James Ogaba, Edosi Oja, Ochigba Ogaba, Ogbu Attah, Anthony Unogwu, Ogaba Obande, Daniel Onogwu da Sunday Otsapa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel