Rikici ya barke tsakanin yan addinin gargajiya da Musulmai a Ogun, Malamin addini ya jigata

Rikici ya barke tsakanin yan addinin gargajiya da Musulmai a Ogun, Malamin addini ya jigata

  • Bayan shekara biyu, yan addinin Oro sun sake kaiwa Musulmai hari
  • Yan addinin gargjiyan sun hana kowa fita da rana saboda suna bikin shekara da suke yi
  • Yan sanda sun damke mutum 3 cikin yan addinin gargajiyan

Ogun - Rikici ya barke ranar Talata a Idi-Iroko, jihar Ogun yayinda wasu yan addinin gargajiyan Oro suka kafa dokar hana kowa fita kuma suka kaiwa Malamin addinin Musulunci hari.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan addinin gargajiyan sun fara taron bautarsu na shekara-shekara ne tun ranar Asabar kuma suka kafa dokar hana mutane fita waje a yankin.

Amma abubuwa suka rincabe lokacin da suka kaiwa Musulmai hari lokacin da ake Sallar Magariba.

Hakazalika an tattaro cewa yan gargajiyan sun jikkata wani Malami, Bola Wasiu, inda ya sha sara a kai.

An ce an garzaya da shi asitibi, tare da wasu mata da yaran da aka kaiwa hari.

Kara karanta wannan

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

Rikici ya barke tsakanin yan addinin gargajiya da Musulmai a Ogun
Rikici ya barke tsakanin yan addinin gargajiya da Musulmai a Ogun, Malamin addini ya jigata

Wannan shine karo na biyu

Wannan shine karo na biyu da za'a kaiwa Masallata a Masallacin Umar Bin Khattab hari.

Shekaru biyu da suka gabata, an kaiwa Masallacin hari.

Limamin Masallacin, Abdul Waliy Omo-Akin, ya ce yan addinin gargajiyan sun saba yarjejeniyar da aka yi da su da sauran addinai cewa su daina abubuwan bokancinsu da rana tsaka.

Yace:

"An jikkata daya daga cikin mambobinmu, Bola Wasiu, don ya fito Sallah da rana."
"Mun samu nasarar damke mutum uku cikin maharan kuma muka mikasu hannun yan sanda."

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

A bangare guda, rikici ya barke tsakanin jama'an yankin Dorayi Babba a jihar Kano da mabiyar kungiyar IMN da aka fi sani da mabiyar akidar Shi'a.

Wannan rikici ya barke ne yayinda yan unguwar sukayi yunkurin hana yan Shi'an gudanar da taronsu 'Ghadeer' a unguwar.

Yan Shi'an sun shirya gudanar da taron ne a kan fili mallakin wani mutumi wanda shima dan Shi'a ne amma aka hanasu.

Kara karanta wannan

Miyagu sun kona motoci kurmus, sun kashe Bayin Allah a Jos bayan rikicin da suka barke

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng