Kotu ta daure wani dodo da ya kai hari ofishin 'yan sandan Najeriya
Wata kotun majistare da ke zaman ta a Makurdi, babban birnin jihar Benuwe, ta tura wasu mutane 10 gidan yari bayan samun su da laifin kai hari ofishin 'yan sandan Najeriya da ke karamar hukumar Ado.
Kotu ta bukaci a ajiye mutanen a gidan yari har sai ta saurari shawarar masana shari'a. Mutanen su ne; Emmanuel Obande, Daniel Ogbu, James Ogaba, Edosi Oja, Ochigba Ogaba, Ogbu Attah, Anthony Unogwu, Ogaba Obande, Daniel Onogwu da Sunday Otsapa.
Rundunar 'yan sannda ta gurfanar da mutane a gaban kotu bisa tuhumarsu da aikata laifuka hudu da suka hada da hada baki domin aikata laifi, yin kutse, yunkurin aikata kisa da aikata ta'addanci.
'Yar sanda mai gabatar da kara, Insifekta Veronica Shaagee, ta sanar da kotun cewa wasu matasa ne fiye da 200, dauke da makamai, suka jagoranci dodon ya kai hari ofishin 'yan sanda da ke Ado. Ta ce dodannin da ake kira "Aketakpa" da sauran matasan sun fito ne daga garin Igumale.
DUBA WANNAN: IGP Adamu ya zayyana dalilai 4 da suka tilasta gwamnati ta haramta kungiyar Shi'a
Ta ce dodannin da matasan na dauke da makamai masu hatsari da suka hada da adda, duwatsu, sanduna da sauransu, sun raunata jami'a 'yan sanda da suka hada da, saja Gabriel Adole, PC Joseph Jato da PC Patrick Lawal. Kazalika, ta yi zargin cewa sun lalata kayan amfanin 'yan sanda a ofishin da kuma wata motarsu kirar Toyota Hilux.
Veronica ta roki kotun ta kara bawa rundunar 'yan sanda domin ta kammala binciken a kan lamarin.
Alkaliyar kotun, uwargida Rose Iyorshe, wacce ta ki sauraron rokon masu laifin, ta bayar da umarnin a tsare su a gidan yari na Makurdi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng