Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci, zai ci gaba da zama a DSS

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci, zai ci gaba da zama a DSS

  • Gwamnatin tarayya ta gaza kawo Nnamdi Kanu gaban kotu saboda wasu dalilai da ba a sani ba
  • Lauyan Nnamdi Kanu ya koka kan yadda aka ki amincewa dangin Kanu su gana dashi yayin da yake tsare
  • An dage karar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba, domin ci gaba da sauraran shari'ar ta Nnamdi Kanu

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta dage shari’ar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar tsageru IPOB saboda gazawar Gwamnatin Najeriya na gurfanar da shi a gaban kotu ranar Litinin, in ji Channels Tv.

Lokacin da aka dago batun, lauya mai gabatar da kara, M. B. Abubakar, ya sanar da kotu cewa an shirya sauraren karar kuma a shirye suke su ci gaba.

Da Dumi-Dumi: An samu cikas, kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Amma lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar da kotu cewa akwai karar da ake jira a gaban kotu don a sauya Kanu daga tsarewar hukumar DSS zuwa cibiyar gyaran hali.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An yi ram da Sowore yayin da ake ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu

Mai shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa ba za a ci gaba da shari’ar ba ba tare da shugaban IPOB din a wirin ba tunda ba shi da damar tsayawa kan shari’ar tasa.

Sai ranar 21 ga watan Oktoba za a sake sauraran shariar Nnamdi Kanu, sannan zai ci gaba da zama a hannun DSS

Kotun ta dage karar zuwa 21 ga Oktoba, 2021, domin ci gaba da sauraren karar, SaharaReporters ta ruwaito.

Ejiofor, babban lauyan Nnamdi Kanu ya fadawa kotu cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta hana dangin Kanu damar ganin sa.

Ya ce:

"An sanar da ni da karfin iko, ina magana daga kotu, cewa an fitar da Nnamdi Kanu daga ikon wannan kotun.
“An hana mu ganawa da Kanu a cikin kwanaki 10 da suka gabata.
"Muna cikin damuwa game da lafiyarsa kuma ba mu san dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta ki kawo shi a kotu ba."

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu

A wani labarin, ‘Yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.

Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.

‘Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.