Rikicin APC a Zamfara: Mun Fi Karfin Kashi 30, Yari Ya Maida Martani Ga Gwamna Matawalle

Rikicin APC a Zamfara: Mun Fi Karfin Kashi 30, Yari Ya Maida Martani Ga Gwamna Matawalle

  • Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul'aziz Yari, ya yi watsi da tayin kashi 30 na mukamai da gwamna Matawalle ya musu
  • Yari yace sam ba zai yiwu ba domin su ne ruhin APC a jihar ko kasonsu yafi tsoka ko a raba dai-dai
  • Ya kuma yi zargin cewa uwar jam'iyya ta ƙasa na kara rura wutar rikicin ta hanyar cigaba da rijistar jam'iyya

Abuja:- Rikicin jam'iyyar APC a jihar Zamfara ya sake ɗaukar sabon babi yayin da ɓangaren tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari da Marafa, suka nuna kin amincewarsu da bukatar gwamna Matawalle.

Tun bayan sauya shekar gwamnan zuwa APC abubuwa ke kara tabarɓarewa a APC, yanzun Matawalle na bukatar a kasafta mukaman jam'iyya da na gwamnatinsa.

Yari ya nuna rashin amincewarsa ne a wani taron manema labarai a Abuja, inda yace sune jigogin APC a jihar don haka su ya kamata a baiwa kaso mafi tsoka ko kuma a raba 50-50.

Kara karanta wannan

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul'aziz Yari
Rikicin APC a Zamfara: Mun Fi Karfin Kashi 30, Yari Ya Maida Martani Ga Gwamna Matawalle Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wace bukata Matawalle ya nema?

A cewar tsohon gwamnan bukatar da aka zo musu da ita na a basu kashi 30 na mukaman jam'iyya da na gwamnati ba abune mai yuwuwa ba.

BBC Hausa ta ruwaito Yari na cewa:

"Matsalar Zamfara fa ba irin matsalar Ebonyi ba ce, ba irin matsalar Kuros Riba ba ce. Jam'iyyar APC a Zamfara tana da komai, tana da gwamna, tana da sanatoci, tana da kowa, abin da ya faru mun sani,"
"Matsayin da muka gabatar wa gwamna Matawalle na raba muƙaman gwamnati da na jam'iyya daidai-wa-daida, shi ne mafi adalci a tsakanin ɓangarorin biyu."

Wake kara ingiza wutar rikicin?

Yari ya kuma zargi uwar jam'iyya ta kasa da kara rura wutar rikicin ta hanyar cigaba da aikin rijistar zama ɗan jam'iyya duk da umarnin kotu.

Yace APC ta aika da tawagar gudanar da rijista a Zamfara duk kuwa da cewa kotu ta haramta hakan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ina Goyon Bayan a Baiwa Yan Kudu Mulkin Najeriya a 2023, Gwamnan Arewa

A cewarsa wasu yan jam'iyya ne suka garzaya kotu bayan shugabancin APC na kasa karkashin gwamna Mai Mala Buni, ya bada umarnin rushe shugabannin APC na Zamfara.

A wani labarain na daban kuma kun ji cewa Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya kai ziyara ga Bola Tinubu a Landan, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Bayan dawowar gwamnan ne ya kira taron manema labarai a gidan gwamnatin Lagos dake Ikeja domin shaidawa mutane abinda ya tattauna da Tinubu a Landan.

Gwamnan yace jigon APC Tinubu yana cikin koshin lafiya ba kamar yadda mutane suke yaɗawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262