Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

  • Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya yi ikirarin cewa jam'iyyar All Progressives Congress tana da goyon bayan Ubangiji
  • Dan siyasar ya bayyana cewa yana farin ciki da shugabancin jam'iyyar kan tsarin rikon kwarya
  • Gwamnan ya yi watsi da shawarar cewa APC na iya samun kanta cikin matsala a nan gaba kan kwamitin da Gwamna Buni ke jagoranta

Abakaliki, Jihar Ebonyi - Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce Allah memba ne na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma Shi ke jagorantar al'amuran jam'iyyar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today.

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne
Gwamna Dave Umahi yace APC na kara karfi Hoto: Governor David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce damar da yankin Kudu maso Gabas ke da shi na samar da shugaban kasa a APC yana hannun Allah.

Yayin da yankin kudu ke ta fafutukar neman kujerar shugaban kasa, babu daya daga cikin manyan jam'iyyun kasar guda biyu - All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) - da ta ayyana yankin da za ta baiwa tikitinta a hukumance.

Sai dai Umahi wanda ya sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a bara, bai bayyana ko APC ta karkatar da kujerar shugaban kasa zuwa shiyyar kudu maso gabas ba.

A kan ko Allah ɗan jam’iyya ne, gwamnan ya amsa da bayar da tabbacin cewa:

“Dan jam'iyya ne. Shi ke jagorantar al'amuran mu. Yana ba da numfashi ga kowane mutum don haka mulki na Allah ne. Duk abin da muke fata zai zo ta wurin Allah ne kawai. Idan Allah ya ce eh, babu wanda zai iya cewa a'a.”

Gwamnan na Ebonyi ya kuma goyi bayan tsarin kwamitin rikon kwarya na APC, yana mai lura da cewa ba a biyan Shugaban riko kuma gwamnan jihar Yobe, Mala Buni.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ce ta kafa kwamitin don yin wani aiki na musamman.

Zaben 2023: Ina Goyon Bayan a Baiwa Yan Kudu Mulkin Najeriya a 2023, Gwamnan Arewa

A gefe guda, yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa, gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi kira da aiwatar da mulkin karba-karba domin kowane yanki ya amfana.

Gwamnan ya yi wannan kira ne ranar Litinin a wata tattaunawa da kafar watsa labarai ta channels tv cikin shirin su na 'Sunrise Daily'.

Wannan na zuwa ne yayin da ake samun karuwar neman a kai wa kudanci mulkin kasar nan a babban zaɓen dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel