Abinda Muka Tattauna da Jagoran APC Bola Tinubu a Birnin Landan, Gwamna

Abinda Muka Tattauna da Jagoran APC Bola Tinubu a Birnin Landan, Gwamna

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya bayyana cewa Bola Tinubu yana cikin koshin lafiya
  • Gwamnan yace sun tattaunawa abubuwa da dama da suka shafi jam'iyyar APC da kuma kasa baki ɗaya
  • Sanwo Olu yace ba shi da masaniyar ranar da jigon APC zai dawo domin shi kaɗai ke da ikon yanke wa kansa

Lagos:- Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo Olu ya bayyana abinda suka tattauna da Bola Tinubu, jagoran APC a birnin Landan.

Dailytrust ta ruwaito manyan mutanen biyu sun gana a Landan yayin da ake jita-jitar Tinubu ba shi da lafiya kuma an kwantar da shi a asibiti.

Amma Gwamna Sanwo-Olu ya shaidawa manema labarai a gidan gwamnati dake Ikeja, cewa yayin ziyararsa sun tattaunawa abubuwa da dama waɗanda suka shafi APC da Tinubu.

Bola Tinubu da Gwamnan Lagos, Sanwo-Olu
Abinda Muka Tattauna da Jagoran APC Bola Tinubu a Birnin Landan, Gwamna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Dagaske ne bashi da lafiya?

Gwamnan ya ƙara da cewa ya ɗauki hotuna da jigon APC ne saboda ya karyata jita-jitar dake yawo cewa an kwantar da shi a asibiti, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Zamfara: Mun Fi Karfin Kashi 30, Yari Ya Maida Martani Ga Gwamna Matawalle

Gwamnan yace:

"Kun ganshi a hotunan, kuma hoto baya ƙarya. Lafiyarsa ƙalau ba abunda ke damunsa, mun yi magana a kan abinda ke wakana a jam'iyyar mu da kuma kasa baki ɗaya."
"Na kai masa ziyara ne domin ingani da idona, kuma domin mutane su kwantar da hankulansu babu wani abun damuwa."

Yaushe zai dawo Najeriya?

Da aka tambayeshi ko sun yi maganar ranar da zai dawo Najeriya, Gwamna Sanwo-Olu ya bada amsar cewa shi kaɗai ne zai iya yanke hukunci kan ranar dawowarsa.

Yace mutum shi ke da ikon yanke lokacin da zai fita kasa da kuma lokacin da ya dace ya dawo.

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari Zata Sake Gyara Matatar Man Kaduna da Warri, Zasu Lakume Dala Biliyan $1.4bn

Majalisar zartarwa ta amince da aikin gyaran matatun man fetur dake Kaduna da kuma Warri wanda zai lakume dala biliyan $1.4bn kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata Cuta Mai Saurin Yaduwa Ta Barke a Sokoto, Ta Hallaka Mutum 23 Wasu 260 Sun Kamu

Bayanin aikin gyaran ya nuna cewa an ware dala miliyan $897m domin gyara matatar mai dake Warri , yayin ta Kaduna zata lakume dala miliyan $586m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262