Karin Bayani: Gwamnatin Buhari Zata Sake Gyara Matatar Man Kaduna da Warri, Zasu Lakume Dala Biliyan $1.4bn

Karin Bayani: Gwamnatin Buhari Zata Sake Gyara Matatar Man Kaduna da Warri, Zasu Lakume Dala Biliyan $1.4bn

  • Gwamnatin tarayya zata sake gyara matatar man fetur dake Kaduna da kuma Warri
  • Karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, shine ya bayyana haka jim kadan bayan fitowa daga taron FEC
  • Najeriya tana da matatar man fetur guda huɗu amma dukkan su basu wani aikin azo a gani

Abuja:- Majalisar zartarwa ta amince da aikin gyaran matatun man fetur dake Kaduna da kuma Warri wanda zai lakume dala biliyan $1.4bn kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Bayanin aikin gyaran ya nuna cewa an ware dala miliyan $897m domin gyara matatar mai dake Warri, yayin ta Kaduna zata lakume dala miliyan $586m, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva shine ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron FEC a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

FG zata sake gyara matatun man fetur
Yanzu-Yanzu: FG Ta Amince da Fitad da Makudan Kudade Domin Gyara Matatar Man Fetur ta Kaduna da Warri Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yaushe za'a fara aikin gyaran matatun?

A cewar ministan aikin gyaran manyan matatun man fetur din zai gudana ne lokaci uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin Ministan yace: "An kasa aikin gyaran matatun man fetur ɗin biyu zuwa kashi uku."

Najeriya na da matatun man fetur huɗu wanda suka haɗa da biyu a Patakwal, amma dukkan su basa aiki yadda ya kamata yayin da ƙasar ke cigaba da shigo da man fetur daga waje.

Shin kwalliya zata biya kuɗin sabulu?

A watan Yuni, Manajan NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa idan aka gyara matatun da Najeriya ke da su tare da matatun dake zaman kansu su fara aiki kamar ta Ɗangote, to Najeriya zata zama babbar ƙasar dake samar da tataccen ɗanyen man fetur.

Ana tsammanin wannan gyaran zai sa matatun su iya samar da adadin man fetur din da yan ƙasa suke bukata.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

Hakanan kyari yace farashin man fetur da yan ƙasa ke sha zai ragu idan aka samu nasara a wajen gyaran da kuma fara aikin masu zaman kansu.

A wani labarin kuma An Cafke Wani Dalibin Jami'a Ya Yi Shigar Mata Ya Zauna Jarabawar Budurwarsa

Wani ɗalibin ƙasar Senagal ya shiga hannu bisa zargin ya yi shigar mata kuma ya zauna wa budurwarsa jarabawa.

Lauyan dalibin ne ya bayyana haka kuma yace ita ma budurwar tasa ta shiga hannun dukkan su a zarginsu da aikata zamba cikin aminci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel