Hotuna da bidiyon mutumin da ya auri mata biyu a rana daya, an yi masu ruwan N20

Hotuna da bidiyon mutumin da ya auri mata biyu a rana daya, an yi masu ruwan N20

  • A karshe dan Najeriya wanda katin gayyatar bikin aurensa ya bazu ya angwance da kyawawan amaransa biyu
  • Sai dai masu amfani da shafukan sada zumunta sun lura cewa baki sun watsa ma ma'auratan kudi ‘yan naira ashirin ashiri a wajen bikinsu
  • Mutane da yawa sun yi mamakin yadda mutumin zai ɗauki nauyin hidindimun mata har biyu

Mutumin Najeriya wanda ya zama abin magana a intanet bayan katin gayyatar bikin aurensa ya bayyana ya auri kyakkyawan amarensa cikin salo.

Mutumin mai shekaru 34 da aka bayyana sunansa da Ekpe Akpove ya auri amaransa a wani daurin biki da aka yi a ranar Lahadi, 15 ga watan Agusta, a jihar Delta.

Hotuna da bidiyon mutumin da ya auri mata biyu a rana daya, an yi masu ruwan N20
Ya angwance da mata biyu a rana daya Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Facebook

Wani bidiyon da sashin Pidgin na BBC ya watsa a Facebook ya nuno lokacin da aka shigar da sabbin ma'auratan cikin filin rawa.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Jos: Sako mai ratsa zuciya da Ahmed Musa ya aikewa gwamnati

Ma’auratan uku sun yi kyau a cikin rigunansu na gargajiya sannan kuma suka sha rawa da kyau. Sun kasance tare da masu yi masu fatan alheri da baƙi waɗanda suma suka yi rawa tare da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi hanzarin lura cewa wadanda suka yi ma ma'auratan likin kudi ba su lika ya wuce ‘yar naira 20 ba.

An gano hakan a cikin bidiyo da hotuna da dama da suka bayyana. Mutumin wanda ya kasance manomi bai damu bah aka ma amaren yayin da dukkansu suka dunga murmushi.

Kafofin sada zumunta sun mayar da martani

Udo Udoma ya ce:

"Ban ga laifin mutumin ba a maimakon haka lafin kyawawan matan 2 na gani da suka bari gaggawa ya dauke tunaninsu duk da sunan aure. Wasu matan na yanzu wasu abu ne daban."

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Liz Evovo ta yi sharhi:

"Sun dade suna zama a tare suna haihuwa tare, abin da suka yi shine karbar sadaki, da kuma karbar haƙƙinsu daga kuniyoyi daban -daban da suke ciki.
"(UTERI OYE ABE REHO) haka nake gani."

Dan Najeriya na shirin angwancewa da kyawawan mata biyu a lokaci guda

A baya mun kawo cewa wani dan Najeriya na shirin angwancewa da mata biyu a rana daya.

Emmanuel Gwatama wanda aka ce abokin angon ne shine ya wallafa hoton katin gayyatar auren mutumin a Facebook.

Da yake bayyana Kome a matsayin gwarzon shekara, Emmanuel ya bukaci abokansa na Facebook da su yi shirin halartar bikin auren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng