Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

  • Daya daga cikin matafiyan da aka kaiwa farmaki a Jos ya bada labarin yadda Kirista ya taimaka masa ya tsira da ransa
  • A cewar matashin, an tare su yayin da ake yunkurin kashe shi amma dan adaidaitan ya bashi hula wacce ya saka yayi basaja
  • Matashin Kiristan mai adaidaita sahu ya umarcesa da ya shiga adaidaitansa inda ya kai shi har masallacin garin Jos

Jos, Filato - Wasu wadanda suka tsallake harin da aka kaiwa matafiya Musulmi a ranar Asabar wurin Gada-Biyu zuwa titin Rukuba dake karamar hukumar Jos ta arewa a jihar Filato, sun bada labarin yadda jami'an tsaro da wasu mutanen kirki suka cece su daga hannun miyagu.

Labarinsu ya bayyana ne bayan da aka gano cewa an sheka mutum 27 a farmakin wanda ya janyo cece-kuce a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi
Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda aka kaiwa fasinjoji 90 dake tafiya a motoci biyar farmaki, maharan da 'yan sanda suka kwatanta da matasan Irigwe da masu goyon bayansu.

Matafiyan sun halarci taron zikirin shekara da kuma murnar zagayowar shekara wanda aka yi a Masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake garin Bauchi.

'Yadda aka cece mu'

Muhammad Ibrahim, daya daga cikin wadanda suka tsira ya sanar da Daily Trust cewa Kiristoci 'yan adaidaita sahu ne suka batar masa da kama inda suka bashi hular hana sallah kuma suka dauke shi daga cikin garin inda suka sauke shi a babban masallacin Jos.

A yayin bada labarin yadda aka kashe matafiya 27, Ibrahim ya ce:

A lokacin da muka isa yankin Gada-Biyu, an samu cunkoso. Hakan yasa muka fara tunanin ko cunkoso ne kamar kowanne amma kafin mu gane komai, mun fara jin duwatsu daga ko ina kuma babu hanyar wucewa saboda sun zagaye motocinmu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jami'an Yan Sanda Na Musamman Sun Ceto Karin Mutum 33 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos

Yankin ya cunkushe, ban san yadda na fito daga mota ba, kawai na ganni a kasa ne kuma ana jifana da duwatsu. Daga nan na ga matukin adaidaita wanda Kirista ne, sai yace in shiga sannan muka tafi.

Wani wanda ya sha da kyar mai suna Ibrahim Jibril, ya sanar da cewa ya samu mafaka a wani daji ne inda ya dinga hangen matasan suna kashe abokan tafiyarsa.

Kowa ya dinga neman mafaka yayin da aka kai mana harin. Na yi sa'ar tserewa zuwa daji. Bayan nan, na ji karar jiniya kuma na san jami'an tsaro ne suka iso. Daga nan ne na fito kuma na tunkari inda sojojin suke muka tafi tare.

Yusuf Adamu, wanda ya samu shigewa wata kwalbati, yace yayi sa'a wayarsa tana hannunsa domin har ya kira wani dan uwansa dake Ekiti wanda ya shawarcesa da kada ya fito har sai jami'an tsaro sun bayyana.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Jos