Gaskiya: Yadda matashi ya mayar da 2500000 da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure

Gaskiya: Yadda matashi ya mayar da 2500000 da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure

  • Wani matashi ya sha yabo bayan da ya mayar da wasu makudan kudade da aka kuskure aka tura zuwa asusunsa
  • Ya bayyana cewa, a ransa bai ji dama yana son cinye kudin ba, don haka ya ji dadi da ya mayar da kudaden
  • Hakazalika 'yan uwansa sun yaba masa tare da jinjina wa da alfahari da kyakkyawan aikinsa

Wani matashi dan Najeriya mai kwatanta gaskiya, Julius Eze, ya sha yabo a kafafen sada zumunta makonni da suka gabata saboda mayar da N2.5m da aka aika zuwa asusunsa, ya kuma fito ya yi magana game da lamarin.

A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi dashi, Julius ya bayyana cewa duk da yana da bukatu a lokacin da aka kuskure tura kudin asusunsa, bai ji a ransa yana son rike kudin ba.

Yadda matashi ya mai da 2500000 da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure
Julius Eze | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Ban yi tunanin rike kudin ba

Ya ce:

“Ban yi niyyar rike kudin ba ko amfani da su don amfanin kaina. Na san ba nawa ba ne kuma babu wanda nasan zai aiko min da irin wannan a lokacin da suka shigo.”

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, Singham ya yi zazzafan martani kan 'yan sanda

Julius ya ce danginsa sun yaba masa kan abin da ya yi, inda ya kara da cewa mahaifinsa ma ya kira don bayyana yadda yake alfahari da kasancewar dansa mai gaskiya kamar sa.

Lokacin da aka tambaye shi kan yadda aka bashi kyauta bisa aikin da ya yi, matashin ya ce mai kudin ya ba shi N50,000, lamarin da ya faranta masa rai matuka.

Ya bayyana cewa an bashi kudin a daidai lokacin da yake cikin matukar bukata. Amma, ya bayyana cewa bai dawo da miliyoyin ba nufin a bashi wani abu ba.

Rashin gaskiya ba shi da kyau

Dangane da yadda ya ji bayan ya dawo da kudin, ya ce:

"Na ji farin ciki sosai da kyau! Na ji na gamsu saboda na san komai arzikin mai kudin, zai shafi kasuwancinsa da kuma lafiyar kwakwalwarsa.”

Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

Kara karanta wannan

Ba a kama ni ba: Saraki ya magantu kan batun kasancewarsa a hannun EFCC

A wani labarin, Alakar kudi a matsayin kadarar musaya mai daraja ya ta'allaka da yadda al'umma ke mu'amalantarsu, a Najeriya ma, batun bai sauya zane ba.

Zai baku sha'awa da matukar burgewa ku san yadda ake hada-hada a shekarun da suka gabata a Najeriya ba tare da kudin takarda ko tsaba ko sulalla ba, da kuma yadda lamarin ya sauya zuwa yanzu.

A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro daga Babban Bankin Najeriya abubuwan da ake huldar cinikayya dasu kafin zuwan kudin takarda da sulalla ko tsaba da kuma yadda aka samar da kudaden da muke kashe wa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel