Da dumi-dumi: Wata babbar jigon PDP ta sauya sheka zuwa APC, ta bayyana dalilanta
- Memba na kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Joy Emordi, ta fice daga jam’iyyarta zuwa APC mai mulki
- A ranar Talata, 3 ga watan Agusta, Emordi tare da wasu mambobin jam'iyyar PDP su 6 sun yi murabus daga babbar jam'iyyar adawar kasar
- A cewarta, PDP ba ta da abin da za ta iya samun nasarar gudanar da mulkin Najeriya da kuma tabbatar da hadin kanta
FCT, Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na ci gaba da cin gajiyar rikicin da ke addabar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Sanata Joy Emordi, daya daga cikin membobi kwamitin PDP bakwai, da suka yi murabus a ranar Talata, 3 ga watan Agusta ta koma APC.
Shugaban Kwamitin Tsare-Tsaren Babban Taron Jam’iyyar APC (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni ya tarbi mai sauya shekar a wani takaitaccen biki a Abuja a ranar Laraba.
Sanarwar da ke tabbatar da sauya shekar daga Darakta Janar na harkokin labaran Shugaban, Malam Mamman Mohammed ya nakalto Sanata Emordi tana cewa ta gamsu da makomar ci gaban Najeriya da hadin kanta na a cikin APC.
Ta bayyana shugaban APC a matsayin mai gaskiya da jajircewa kan hadin kan Najeriya tare da tsare-tsare don makomar wadanda za su zo nan gaba.
Da take ba wa shugabannin APC tabbacin biyayya da goyon baya Emordi ta ce:
"Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC tana yi wa Kudu maso Gabas aiki kuma wannan yana jawo karin membobin PDP zuwa APC."
Buni ya nuna farin cikinsa da shawarar sanatar na bayar da gudummawa ga hadin kan kasar.
Buni ya ce :
"Akwai bukatar mu hada hannu don daidaita siyasa da hadin kan kasarmu.”
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewaa ya bayar da tabbacin cewa zuwan Sanata Emordi da sauran fitattun 'yan siyasa daga kudu maso gabas APC zai inganta hadin kan kasa.
Ya kara da cewa:
“Kudu maso Gabas yankin siyasa ne mai karfin gaske kuma yana da matukar muhimmanci ga hadin kan kasar, wannan babu shakka zai kara hada kan kasa."
APC za ta fadi zaben Shugaban kasa a 2023: Shahararren malamin addini ya yi hasashe
A wani labarin, Shahararren malamin addini, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki za ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023.
Ayodele ya fadi haka ne a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, inda ya ce hasashensa zai zama gaskiya idan ba a magance matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ba.
Asali: Legit.ng