APC za ta fadi zaben Shugaban kasa a 2023: Shahararren malamin addini ya yi hasashen

APC za ta fadi zaben Shugaban kasa a 2023: Shahararren malamin addini ya yi hasashen

  • Babban fasto, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi jam’iyyar APC gabanin zaben shugaban kasa na 2023
  • Faston ya ce APC za ta fadi zaben shugaban kasa idan ba a magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu ba
  • Ya bayyana cewa za a yi gagarumin tashin hankali game da magudin zabe a kasar nan a 2023

Shahararren malamin addini, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki za ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023.

Ayodele ya fadi haka ne a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, inda ya ce hasashensa zai zama gaskiya idan ba a magance matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ba.

APC za ta fadi zaben Shugaban kasa a 2023: Shahararren malamin addini ya yi hasashen
Primate Elijah Ayodele ya ce APC za ta fadi zaben shugaban kasa a 20923 Hoto: INRI Evangelical Spiritual Church, Achievers Cathedral, Lagos
Asali: Facebook

Malamin ya ce 'yan Najeriya sun gaji da jam'iyya mai mulki kuma suna bukatar gyara duk dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta, jaridar PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

Ya kuma yi hasashen cewa talakawa za su yi tawaye kan magudin zabe a 2023 kamar yadda ya gaya wa jam'iyyar da ta yi hanzarin daukar mataki.

Malamin ya fadawa shugabannin APC da su magance matsalolin shari’a da jam’iyyar ke fuskanta domin kada a sauke su daga kujerar shugaban kasa bayan zaben 2023.

A zaben da ke tafe a Anambra, Primate Ayodele ya tsaya tsayin daka kan maganarsa cewa jam’iyya mai mulki ba za ta yi nasara ba, jaridar Daily Post ta ruwaito.

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

A wani labari na daban, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce Allah memba ne na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma Shi ke jagorantar al'amuran jam'iyyar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today.

Kara karanta wannan

A karshe tsohon Shugaban INEC ya yi watsi da APC da PDP, ya shiga PRP, ya bayyana dalilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel