Fitacciyar jigon jam'iyyar APC ta sauya sheka, ta koma PDP

Fitacciyar jigon jam'iyyar APC ta sauya sheka, ta koma PDP

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta rasa daya daga cikin jigonta dake jihar Benue inda ta koma PDP
  • Mai sauya shekar, Mimi Adzape-Orubibi, a ranar Talata tace jam'iyya mai mulki ba za ta bada damar cikar burinta ba
  • Adzape-Orubibi tace yadda ake neman mulki tare da tsananin da 'yan kasa suka shiga yana daga cikin dalilan da suka sa ta sauya sheka

Kwande, Benue - Mimi Adzape-Orubibi, tsohuwar 'yar takarar kujerar Sanata karkashin inuwar jam'iyyar APC a jihar Benue, ta mika wasikar barin jam'iyyar mai mulki.

A ranar Talata, 3 ga watan Augusta, Adzape-Orubibi ta sanar da The Sun cewa ta tura sanarwa a rubuce ga shugaban jam'iyyar na gundumar Kumakwagh dake karamar hukumar Kwande ta jihar, Honarabul Terwase Aheeve.

KU KARANTA: Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki

Fitacciyar jigon jam'iyyar APC ta sauya sheka, ta koma PDP
Fitacciyar jigon jam'iyyar APC ta sauya sheka, ta koma PDP. Hoto daga Mimi Adzape-Orubibi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe

Kara karanta wannan

Siyasa: Atiku ya fara kyakkyawan shirin kamfe don karbe mulkin Najeriya a 2023

Mene ne dalilinta na barin jam'iyyar mai mulki?

Kamar yadda jigon jam'iyyar APC tace, ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gane cewa jam'iyyar mai mulkin ba zata bata damar cikar burinta ba.

Ta kara da kafa dalili da lalacewar tsaro, tabarbarewar tattalin arziki a kasar nan da kuma rashin daidaituwar da ake ta samu a shugabancin jam'iyyar mai mulki.

A yayin jawabi kan hukuncinta, ta ce:

Na fi duban tsarin siyasa kuma na yadda cewa siyasa ta zama zabin jama'a mai amfanar jama'a. Hakan ne yasa nake neman inda zan yi siyasar jama'a.
Bani da matsala da kowanne mutum a kan abinda suka yi ko suka kasa yi ko a lokacin da nake APC. Wannan hukunci na ne, kuma saboda jama'a ne nake yi.

Mai Shari'a Garba, babban alkalin FCT yayi murabus, ya bayyana dalili

Sabon babban alkalin FCT, Justice Salisu Garba ya yi murabus da kanshi bayan an nadashi a matsayin mai gudanarwa na NJI.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223

An samu wannan sanarwar ne a wata takarda wacce hadimin CJN na fannin yada labarai, Ahuraka Isah ya gabatar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewarsa, NJIBG, Karkashin shugabancin babban alkalin Najeriya, CJN, Justice Tanko Muhammad, ta amince da nadin Garba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: