Labari da Duminsa: Kotu Ta Bada Belin Mataimakan Sunday Igboho

Labari da Duminsa: Kotu Ta Bada Belin Mataimakan Sunday Igboho

  • Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta amince da bada belin hadiman Sunday Igboho 12
  • Kotun ta bada wannan umarnin ne bayan sauraron kowane ɓangare yayin zamanta na yau
  • Lauyan DSS ya nemi kotun ta bada belin 8 daga ciki amma huɗu akwai sauran bincike a kansu

FCT Abuja:- Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta amince da bukatar beli da aka gabatar gabanta na hadimann Sunday Igboho 12 da DSS ta kame, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mai shari'a Obiora Egwuatu, ya bada umarnin a saki baki ɗaya hadimai 12 dake tsare a hannun DSS, kamar yadda channls tv ta ruwaito.

Alkalin ya bada wannan umarnin ne bayan dawowa daga wani hutu da aka shafe sama da awa ɗaya, biyo bayan kotu ta saurari kowane ɓangare.

Lauyan mataimakan Igboho, Pelumi Olajengbesi, ya nemi kotu ta bada belin waɗanda yake karewa ba tare da wasu sharuddai ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Mataimakan Igboho 12 a Kotu
Labari da Duminsa: Kotu Ta Bada Belin Mataimakan Sunday Igboho Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin ɓangaren DSS Sun amince da belin?

Lauyan hukumar DSS, I. Awo, ya shaidawa kotun cewa baya jayayya da bada belin 8 daga cikinsu.

Amma lauyan yace yana ja da bada belin sauran mutum 4 saboda binciken DSS ya nuna cewa suna da hannu dumu-dumu a laifin shigo da makamai.

Lauyan ya ƙara da cewa bai kamata a bada belin waɗannan huɗun ba idan har adalci za'a yi kuma za'a duba yanayin tsaron ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa a hakan ma DSS ba ta gama bincike a kansu ba, tana cigaba da bankaɗo laifinsu.

Awo ya tabbatarwa kotu da cewa da zaran hukumar DSS ta kammala bincike a kansu ba zata yi wata-wata ba zata gurfanar da su a Kotu.

A jawabin lauyan yace:

"Abinda muke gudu shine idan aka bada belinsu ba zasu rinka kawo kansu domin cigaba da bincike ba da kuma yuwuwar sake gurfanar da su."

Kwana 34 suna tsare, An tauye musu yanci

Kara karanta wannan

Karin Bayani: DSS Ta Bi Umarnin Kotu, Ta Gabatar da Dukkan Hadiman Sunday Igboho a Kotu

Lauyan dake kare hadiman Igboho, Olajengbesi, ya bukaci kotu da ta yi watsi da dalilin lauyan DSS saboda basa cikin dokar ƙasa.

Lauyan ya kara da cewa an tsare mutanen na tsawon kwanaki 34 ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu da wani laifi ba.

Yace cigaba da kulle su ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasar nan kuma tauye musu hakkinsu ne.

Olajengbesi yace DSS ba ta bukatar kwanaki 34 domin binciken mutanen da tace ta kama da manyan makamai.

A wani labarin kuma Wasu Yan Daba Sun Gutsire Kan Dalibin Kwalejin Fasaha a Kwara

Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka kashe ɗin ɗan wata kungiyar daba ne dake adawa da makasan.

Har zuwa yanzun ba'a gano gangar jikin ɗalibin ba, amma yan sanda suna cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel