Da Dumi-Dumi: Wasu Yan Daba Sun Gutsire Kan Dalibin Kwalejin Fasaha a Kwara
- Wasu yan ƙungiyar daba sun kashe wani ɗalibin kwalejin fasaha ta jiha a Kwara
- Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka kashe ɗin ɗan wata kungiyar daba ne dake adawa da makasan
- Har zuwa yanzun ba'a gano gangar jikin ɗalibin ba, amma yan sanda suna cigaba da bincike
Kwara:- Wasu da ake zargin yan ƙungiyar daba ne sun kashe ɗalibin kwalejin fasaha ta jihar Kwara mai suna, Olawale.
Dailytrust ta ruwaito cewa yan daban, waɗanda suke ƙungiyar adawa, sun farmake shi ne jim kaɗan bayan ya bar gida ranar Talata.
An gano kan ɗalibin a shataletalen Unity a Ilorin bayan mahaifiyarshi ta shafe awanni tana neman ɗan nata.
Har yanzun da muke kawo muku wannan rahoton ba a gano gangar jikinsa ba sai dai kan kaɗai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahotan this day ya bayyana cewa ɗalibin sanannen mai gyaran waya ne a babbar kasuwar gyaran waya dake Ilorin.
A cewar mahaifiyarsa, dake cikin wani yanayi na damuwa:
"Olawale ya bar gida karfe 8:00 na safe ta wuce ranar Litinin da safe, amma da naga bai dawo ba a lokacin da ya saba na dinga kiran wayarsa bai daga ba."
"Daga baya sai muka yanke hukuncin kai rahoton ɓatarsa caji ofis daga nan kuma muka je makarantarsu muka duba asibiti ko tsautsayin hatsari ya rutsa da shi."
"Muna cikin nemansa ne sai muka ga mutane sun tattaru a wani wuri suna ɗaukar hotuna a Unity. Ba zato sai naga ashe kan ɗana da muke nema ne."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Da aka tuntubi mai magana da yawun yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ranar Laraba, yace jami'ai na cigaba da kokarin kama waɗanda suka aikata kisan.
Mr. Okasanmi yace:
"Yayin da muka amsa wani kira, mun gano kai babu gangar jiki a ɗaya daga cikin yankin dake da kalubale a Ilorin ranar Talata."
"A binciken da muka yi zuwa yanzun mun gano cewa aikin yan daban kungiyar asiri ne."
"Wanda aka kashe ma ana zargin ɗan wata kungiyar daba ne kuma ɗalibin kwalejin fasaha ne. A halin yanzu muna cigaba da bincike."
Fusatattun ɗalibai sun toshe babbar hanya a Ondo
A wani labarin kuma Fusatattun Daliban Wata Jami'an Sun Toshe Babbar Hanya Saboda Sheke Dan Uwansu
Wasu fusatattun ɗalibai na jami'ar fasaha ta tarayya dake Akure (FUTA), jihar Ondo, sun toshe babbar hanyar Akure-Ilesa, kamar yadda punch ta ruwaito.
Rahoto ya nuna cewa ɗaliban sun ɗauki wannan matakin ne domin zanga-zangar kashe ɗan uwansu ɗalibi, wanda ya mutu a sanadin hatsari ranar Litinin da yamma.
Asali: Legit.ng