Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili

Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili

  • Babban Lauya, kuma dan rajin kare hakkin dan adam Femi Falana, ya nemi a mika Kyari ga FBI
  • Ya ce, ya kamata rundunar 'yan sanda ta yi bincike mai zurfi sannan ta kai Kyari Amurka a bincikeshi
  • Ya bayyana haka yayin da aka tambaye shi ra'ayinsa game da dambarwar da ake zargin Abba Kyari akai

Shahararren lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan adam, Cif Femi Falana (SAN) ya yi kira ga Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya aiwatar da bukatar Amurka ta mika mata Abba Kyari akan ka'ida.

Kyari, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Borno, kwanan nan ne Hukumar Bincike ta FBI, wata hukumar tabbatar da doka a Amurka ta zarge shi da hannu a wata harkallar damfara.

Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfarar wani hamshakin attajiri, ya furta cewa ya ba Kyari cin hanci don kamo wani da ya nemi ya zarce shi a zambar dala miliyan 1.1.

Kara karanta wannan

Ofishin Abubakar Malami ya magantu kan zargin da ake wa Abba Kyari

Wannan fallasa ta girgiza 'yan Najeriya da yawa kamar DCP Kyari kafin yanzu, wanda aka fi sani da Jarumin Dan Sanda na Najeriya.

Babban lauya ya ce akwai bukatar mika Abba Kyari ga FBI, ya fadi dalili
Femi Falana (SAN) | Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

A matsayinsa na Shugaban Rundunar Bayar da Bayanan Sirrin 'Yan Sanda (IRT), tawagar Kyari ta kware wajen cafke dimbin masu aikata laifuka a cikin kasar wanda hakan ya ba shi yabo a zaman majalisa na musamman daga Majalisar Wakilan Najeriya.

Falana ya ce dole ne Najeriya ta mutunta yarjejeniyar kasa da kasa

Falana ya ce Kwamitin Bincike na Musamman da Babban Sufeto Janar ya kafa Babban Sufeto kan lamarin da ake dubawa ya kamata ya yi cikakken aiki.

Da yake magana yayin wata hira ta wayar tarho da gidan Talabijin na Afirka mai zaman kansa wanda jaridar Daily Sun ke sa ido, Falana ya bayyana cewa Kyari ya samu ne daga tsarin gwamnatin da ya gaza.

A kalmomin sa yake cewa:

"Don kawo karshe da rufe wannan mummunan babi, binciken dole ne ya wuce tuhumar da FBI ta yi, dole ne a bincika lamarin a cikin gida, kuma ba wai a mika Kyari ga Amurka kawai ba.

Kara karanta wannan

FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili

"Muna aiki a karkashin doka ko gwamnati ta so ko ba ta so, akwai dokar mika mutum wanda kasashe kamar Amurka da Najeriya suka kulla yarjejeniya da su.
"Don haka akwai hanyoyin da za a bi idan ana son wanda ake zargi da laifi a nan ko a Amurka ya fuskanci shari'ar kotu.
“Game da Najeriya-Amurka, an shiga yarjejeniya a 1935 karkashin mulkin mallaka na Burtaniya, kuma tsakanin lokacin zuwa yanzu, an mika dimbin 'yan Najeriya, wasu an karbe su an jefar dasu a Amurka, amma ba ko guda daya, wanda ake zargi Ba'amurke da aka kawo shi kotu a Najeriya.”

FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili

Babban Lauyan Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), ya ce tilas Amurka ta gabatar da bukatar neman a mika mata mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari ta hanyar da ta dace.

Cibiyar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ne ta zargi Kyari a wata tuhumar zamba da Ramon Abbas wanda kuma ake kira Hushpuppi ke fuskanta a Amurka.

Kara karanta wannan

Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

Tuhumar Kyari ta biyo bayan umurnin kama shi daga wata kotun Amurka a gundumar tsakiyar California.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Ozekhome ya ce hukumar FBI ba ta da ikon zuwa Najeriya haka kawai don kama Kyari ba tare da bin ka’ida ba, Arise Tv ta ruwaito.

Babban Kamu: FBI ta kwamuso wasu 'yan Najeriya da ke damfara a kasar Amurka

A wani labarin, an cafke wasu 'yan Najeriya biyu a Amurka kan zargin damfara da sauran laifuka da suka kunshi dala dubu 25 kan kudaden tallafin da ake bai wa marasa aiki.

Jaridar Premium Times a rawaito cewa mutanen biyu da suka hada da Olushola Afolabi da Olugbeminiyi Aderibigbe ana zarginsu da damfarar ma'aikatar tsaron ma'aikata da gwamnatin Amurka ta shirin inshorar tallawa masara aikin yi.

An gano suna aiwatar da damfarar ne ta hanyar takardun shaidar bogi da suka kirkira wanda ke basu damar tura milyoyin daloli na tallafin marasa aiki zuwa wani asusun banki da suke kula da shi.

Kara karanta wannan

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

Asali: Legit.ng

Online view pixel