Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

  • Kwamitin da aka kafa na musamman domin binciken Abba Kyari ya fara aiki
  • DIG Joseph Egbunike da sauran jami’ai uku za su binciki babban ‘dan sandan
  • IGP ya bada shawarar a dakatar da Abba Kyari daga aiki yayin da ake bincike

Abuja - Sakamakon shawarar da umarnin da Sufetan ‘yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba ya bada a baya, kwamiti ya soma binciken DCP Abba Kyari.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman da zai zauna domin ya binciki zargin da ake yi wa daya daga cikin jami’anta, Kyari.

Jaridar Tribune ta ce hakan na zuwa ne bayan Hukumar FBI ta zargi jami’in da karbar cin hanci da taimaka wa Ramon Azeez wajen damfarar wani mutum.

Shugaban sashen hulda da ‘yan jarida da wayar da kan al’umma na hukumar PSC mai kula da aikin ‘yan sanda, Ikechukwu Ani, ya bada wannan sanarwa.

Mista Ikechukwu Ani ya ce hukumar ta umarci Sufetan ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya taimaka mata da duk wasu bayanai da za su taimaki binciken.

Kara karanta wannan

Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan

Da ya ke jawabi a birnin tarayya Abuja, Ani ya bayyana cewa Abba Kyari ba zai koma aiki ba har sai an kammala wannan bincike, sannan zai san matsayarsa.

Abba Kyari
DCP Abba Kyari Hoto: www.ghanaweb.com
Asali: UGC

TheCable ta samu labari cewa ba za ayi tunanin mika Kyari ga gwamnatin Amurka ba, har sai ‘yan sanda sun kammala gudanar da na su binciken na cikin gida.

Joseph Egbunike zai shugabanci kwamitin SIP

DIG Joseph Egbunike wanda ya ke rike da sashen FCID mai binciken masu manyan laifuffuka shi ne zai jagoranci wannan kwamiti na musamman da aka kafa.

Rahoton ya nuna kwamitin SIP za su binciki duk zargin da hukumar FBI ta kasar Amurka ta jefi jami’in tsaron da su, ta kuma bibiyi takardun da aka fitar da su.

Ragowar mutum uku ‘yan kwamitin za su taimaka wa DIG Egbunike, bayan sun kammala binciken, za su gabatar da abin da su ka gano da shawararinsu.

An yi waje da Abba Kyari, an nada wani a madadinsa

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

A makon jiya aka dakatar da DCP Abba Kyari daga bakin aiki, DCP Tunji Disu ne ya gaje shi a matsayin shugaban dakarun IRT masu tattara bayanan sirrri.

IGP ya ce Disu zai rike Rundunar IRT yayin da ake binciken zargin da ake yi wa Kyari. Usman Alkali Baba Disu zai shiga ofis ba tare da wani bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel