FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili

FBI ba ta da ikon kame Abba Kyari, babban lauya Mike Ozekhome ya fadi dalili

  • Wani babban lauya a Najeriya ya caccaki FBI kan umarnin kame jami'in dan sanda Abba Kyari
  • Lauyan ya ce, FBI ba ta da ikon tasa keyar Abba Kyari zuwa Amurka ba tare da bin ka'ida ba
  • Ya bayyana yadda ya kamata Amurka ta bi a hankali wajen gabatar da tuhuma yadda ya dace

Babban Lauyan Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), ya ce tilas Amurka ta gabatar da bukatar neman a mika mata mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari ta hanyar da ta dace.

Cibiyar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ne ta zargi Kyari a wata tuhumar zamba da Ramon Abbas wanda kuma ake kira Hushpuppi ke fuskanta a Amurka.

Tuhumar Kyari ta biyo bayan umurnin kama shi daga wata kotun Amurka a gundumar tsakiyar California.

FBI ba isa ta kame Abba Kyari ba, babban lauya Mike Ozekhome ya caccaki Amurka
Babban Lauya, Mike Ozekhome | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake mayar da martani kan lamarin, Ozekhome ya ce hukumar FBI ba ta da ikon zuwa Najeriya haka kawai don kama Kyari ba tare da bin ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Kwamitin jami'an tsaro mai mutum 4 da zai binciki Abba Kyari ya fara aiki bayan dakatarwa

Ya shaida wa Arise News a ranar Litinin, 2 ga Agusta cewa:

"Lokacin da Amurka ta nemi Abba Kyari, na ji mutane suna cewa FBI na da ikon kama Abba Kyari. A'a, ba zai yiwu a iya yin hakan ba. Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta komai raunin da muka shiga.
“FBI ba ta da ikon zuwa nan haka kawai ta dauki Abba Kyari. Dole ne a bi tsarin fitar da mutane kamar yadda aka fada a cikin Dokar Kaddamar da Dokokin Tarayyar Najeriya ta 2004. Dole ne a duba Sashe na 2, 4, 5, 6, 7, 8, da 9 na dokar da aka yi.

Da yake karin haske, Ozekhome ya yi nuni da cewa wannan ba shine karon farko da Najeriya za ta fuskanci shari'ar tasa keyar wani dan ta ba.

Amma, ya koka da cewa batutuwan da suka shafi Kyari, dan awaren Yarabawa, Sunday Igboho, da jagoran haramtacciyar kungiyar aware ta IPOB, Nnamdi Kanu duk sun faru ne a lokaci guda.

Kara karanta wannan

Sabon Bincike: Yadda Hushpuppi ya aika wa Abba Kyari miliyoyi na wata harkalla

Amurka ba ta da ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

Biyo bayan takaddamar da aka samu daga rahoton Amurka da ke tuhumar Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DSP), Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda (PSC) a ranar Asabar, 31 ga Yuli ta yi martani kan takaddamar.

Vanguard ta ruwaito cewa hukumar ba ta sami rahoto na doka ba kuma mai ma'ana kan "bakon" zargin na Amurka mai umarnin kama Abba Kyari.

Legit.ng ta tattaro cewa PSC ta yi kira ga ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da ya jagorance ta kan batun tunda ita (hukumar) ita ce hukumar da ke da ikon ladabtar da jami'an 'yan sanda da suka yi kuskure.

Babban Kamu: FBI ta kwamuso wasu 'yan Najeriya da ke damfara a kasar Amurka

A wani labarin, an cafke wasu 'yan Najeriya biyu a Amurka kan zargin damfara da sauran laifuka da suka kunshi dala dubu 25 kan kudaden tallafin da ake bai wa marasa aiki.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

Jaridar Premium Times a rawaito cewa mutanen biyu da suka hada da Olushola Afolabi da Olugbeminiyi Aderibigbe ana zarginsu da damfarar ma'aikatar tsaron ma'aikata da gwamnatin Amurka ta shirin inshorar tallawa masara aikin yi.

An gano suna aiwatar da damfarar ne ta hanyar takardun shaidar bogi da suka kirkira wanda ke basu damar tura milyoyin daloli na tallafin marasa aiki zuwa wani asusun banki da suke kula da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel