Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari

Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari

  • Hotuna da bidiyoyin wankan amarya, Gimbiya Zahra Bayero da Yusuf Muhammadu Buhari sun fara bayyana
  • A bidiyoyin da hotunan, an ga zukekiyar gimbiyar sanye da rigar alfarma yayin da kasaitattun kawayenta ke kewaye da ita
  • Walkiya, kyalli, kyau, izza da kasaitar tsuleliyar amaryar ya cika ko ina yayin da take sanye da farar riga mai hannayen raga

Kano - Alamu bayyane suke na cewa tuni aka fara shagalin bikin gidan shugaban kasa da na gidan sarautar Bichi.

Tun a ranar Asabar da ta gabata Legit.ng ta fara kawo muku kyawawan hotunan wasan Polon da aka yi a ranar Juma'a da ta gabata na bikin diyar Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Bayero da dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari.

Bidiyoyi da hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari
Bidiyoyi da hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari. Hotuna daga @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

KU KARANTA: Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe

A yau kuwa Legit.ng ta tattaro muku tsula-tsulan hotuna da bidiyoyin wankan amarya, wanda a zamanance aka mayar da shi liyafa mai zaman kanta da ake kira da Bridal Shower.

Kara karanta wannan

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

A cikin bidiyoyin da hotunan da shafin @arewafamilyweddings suka wallafa, an ga kyakyawar gimbiyar tare da kawayenta suna ta daukan hotuna yayin da sauti mai dadi ke tashi.

Ya kwalliyar amarya da kawayenta ta bayyana?

A hotunan, da bidiyon, an ga tsuleliyar amaryar sanye da farar riga mai hannuwan raga yayin da kawayenta ke sanye da riguna farare na ankon da aka yi shi domin wankan amaryan.

Walkiya, kyau tare da izzar amarya jinin sarauta, ta cika wurin da ake liyafar, duk da dai kawayenta da kallo daya zaka musu ka san 'ya'yan wane da wance ne suma ba a bar su a baya ba.

KU KARANTA: Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda

Innalillahi: Allah ya yi wa mahaifiyar Aminu Alan Waƙa rasuwa

Daga Allah muke, gareshi zamu koma! Allah yayi wa mahaifiyar fitaccen mawaki Aminuddeen Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waka, rasuwa.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

An haifa Hajiya Bilkisu Sharif a shekarar 1921 kuma ta koma ga mahaliccinta a shekarar 2021.

Kamar yadda Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram a daren ranar Litinin, Hajiya Bilkisu ta rasu ta bar 'ya'ya 2 da jikoki 25.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel