Innalillahi: Allah ya yi wa mahaifiyar Aminu Alan Waƙa rasuwa
- Allah yayi wa mahaifiyar shahararren mawaki, Aminuddeen Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan waka rasuwa
- Hajiya Bilkisu Sharif ta rasu tana da shekaru 70 cif a duniya inda ta bar 'ya'ya biyu da jikoki 25 a duniya
- Za a yi jana'izarta da karfe tara da rabi na safiyar Talata kamar yadda jarumi Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram
Daga Allah muke, gareshi zamu koma! Allah yayi wa mahaifiyar fitaccen mawaki Aminuddeen Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waka, rasuwa.
An haifa Hajiya Bilkisu Sharif a shekarar 1921 kuma ta koma ga mahaliccinta a shekarar 2021.
KU KARANTA: Ali Kachalla: Waye Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF?
KU KARANTA: Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe
Kamar yadda Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram a daren ranar Litinin, Hajiya Bilkisu ta rasu ta bar 'ya'ya 2 da jikoki 25.
Aminuddeen Ala da Khadija Ladan sune 'ya'yan da ta bari.
Kamar yadda sarki ya wallafa, za a yi jana'izarta a yau ranar Talata, 3 ga watan Augusta da karfe 9 da rabi na safe.
Allah yaji kanta da Rahama, ya kyautata makwanci, yasa mu cika da kyau da imani idan tamu ta zo. Ameen.
Bayan farmakin Kareto, sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Gubio, sun yi barna
Bayan farmakin Kareto, sojojin Najeriya sun sake shiryawa tare da kai babban farmaki kan mayakan ta'addanci na Boko Haram dake Gubio, PRNigeria ta ruwaito.
Miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun ji ruwan wuta bayan dakarun sojin Najeriya sun bankado maboyarsu dake Gubio a jihar Borno a ranar Lahadi.
An gano cewa a ranar Asabar ne 'yan Boko Haram suka kaiwa wata tawagar sojoji samame kan babbar hanyar Gubio zuwa Damasak dake yankin Kareto a arewacin jihar Borno.
Duk da ba a san yawan rayukan da suka salwanta ba a bangaren dakarun sojin, amma kamar yadda majiyar tsaron ta sanar, ta ce cike da dabara sojojin suka tsara yadda zasu kai farmaki maboyar miyagun a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng