Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki

  • Usman Kyari, kanin Abba Kyari, ya saba wallafa hotunansa cikin sutturun alfarma da tsula-tsulan motoci
  • Hankali ya fara komawa kan Usman Kyari ne bayan da dan damfarar yanar gizo yace ya baiwa yayansa cin hanci
  • A shafin Usman mai mabiya sama da 2,000, akwai tsula-tsulan hotunan inda ya dauka cike da ado tare da bayyanar dukiya

Damaturu, Yobe - Usman Kyari, kanin Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda, ya zama a saman kanun labarai bayan jama'a sun kyalla ido sun ga irin hotunan rayuwarsa da yake wallafawa a shafinsa na Instagram.

Hankali ya koma kan Usman ne bayan Hushpuppi, wanda aka fi sani da Ramon Abbas, ya ce ya baiwa Abba Kyari wasu makuden kudaden domin ya kama wani dan damfara abokin hamayyarsa.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Abba Kyari ya saba wallafa yanayin rayuwarsa a Instagram

Kafin aukuwar wannan lamarin, an san babban dan sandan da zama koyaushe a kafar sada zumunta ta Instagram.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan baya wallafa hotunan jarumtarsa a yayin da yake ragargazar 'yan ta'adda, toh tabbas za a ganshi ya choge cikin 'yan uwansa, manyan 'yan siyasa da fitattun jama'a, thecable ta ruwaito.

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ali Kachalla: Waye Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF?

Kamar dakataccen dan sandan, shafin Usman na Instagram dankare yake da son shanawa tare da fantamawa cikin arziki karara, thecable ta ruwaito

Daga daukan hotuna cikin jerin motocin alfarma zuwa sanya kayan alfarma na sutura, shafinsa yana da mabiya sama da 2,000 na masu son ganin kyale-kyale.

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa

An hana mu ganin Nnamdi Kanu, Lauyan shugaban IPOB ya koka

Daya daga cikin lauyoyin Nnamdi Kanu ya ce an hanasu ganin shugaban IPOB. Kanu wanda yanzu haka yana hannun SSS a Abuja bisa umarnin kotu, Premiumtimes ta wallafa.

Lauyansa, Aloy Ejimaker ya ce a ranar Alhamis sun hana shi da sauran lauyoyin Kanu biyu daga ganinsa duk da kotu ta basu damar ganinsa duk wata Litinin da Alhamis.

A cewarsa a lokacin da shi da sauran lauyoyin suka kai masa ziyara inda aka tsare shi, sun yi matukar mamakin yadda jami’an tsaron suka murje ido suka hanasu ganin shi duk da sun san dalilinsu na zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel