Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223
- Dakarun sojin Najeriya na cigaba da kokarin ganin bayan ta'addanci da ya addabi arewacin Najeriya
- Operation HADARIN DAJI ta yi nasarar sheke 'yan bindiga 14, damke masu kai wa miyagu bayanai 16 da ceto dabbobin sata 223
- Rundunar ta sanar da yadda ta ceto mutum 36 kuma ta taimakawa wata mata mai juna biyu ta haihu lafiya
Arewa maso yamma - A cikin kankanin lokaci, rundunar soji ta Operation HADARIN DAJI ta dinga kai samame tare da ceto jama'a ta hanyar amfani da jiragen yaki da kuma taimakon dakarun sojin kasa.
Wannan ayyukan sun dinga yin su ne lokaci daya a wurare daban-daban na yankin arewa maso yamma, kuma ana samun manyan nasarori, prnigeria ta ruwaito
KU KARANTA: Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna
KU KARANTA: Ango dake aiki kan na'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce
Wuraren da dakarun suka yi aiki
A cikin wannan lokacin, dakarun sun amsa wani kiran gaggawa wanda aka sanar dasu cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki kauyen Hanutaru da na Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, kan babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto.
Har ila yau, dakarun da suka gaggauta zuwa ceto a wani farmaki da miyagun suka kai karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, kauyen Eldabala dake Tangaza da kuma kan babban titinin Lamba Bakura zuwa Dogo Karfe dake jihar Sokoto.
Nasarorin da aka samu
Daga cikin nasarorin da suka samu, sun sheke miyagun 'yan bindiga goma sha hudu. Sun ceto mutane talatin da shida da aka yi garkuwa dasu kuma sun taimakawa daya daga cikin wurin haihuwa cikin koshin lafiya.
Kamar yadda prnigeria ta wallafa, an samu bindigogi kirar AK-47, babura shida, kayan sojoji da na 'yan sanda, ababen hawa shida da adduna hudu.
Hakazalika, an damke miyagu ashirin da hudu wadanda suka hada da masu kaiwa 'yan bindiga bayanai su goma sha shida da kuma wani dan basaja mai suna Faisal Saidu wanda ke bayyana sunansa Lance Corporal Saidu Abubakar.
An samu nasarar kwato dabbobin da 'yan bindiga suka sata guda 223 duk a cikin wannan lokacin.
Miyagu sun sako sarkin Jaba
Miyagun 'yan bindiga sun sako babban basaraken jihar Kaduna, Danladi Gyet Maude, wanda aka sace a jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito muku yadda aka sace basaraken a ranar Litinin yayin da yaje duba gonarsa dake Panda a jihar Nasarawa.
Amma wata majiya daga fadar ta sanar da Daily Trust cewa an sako basaraken a ranar Laraba wurin karfe tara da rabi na dare.
Asali: Legit.ng