Siyasa: Atiku ya fara kyakkyawan shirin kamfe don karbe mulkin Najeriya a 2023

Siyasa: Atiku ya fara kyakkyawan shirin kamfe don karbe mulkin Najeriya a 2023

  • Gabanin zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci wani gwamna domin neman goyon baya
  • Ya kai ziyarar ne a jihar Ribas domin neman karbuwa a yankin kudu, wanda ya nema daga gwamna Wike
  • Wannan na zuwa ne daga wata majiyar da ta fito daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya

Jihar Ribas - Rahotanni daga jaridar Sun na nuni da cewa gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, yana shirye-shirye sosai don taka rawa gada-gadan.

Jaridar ta yi ikirarin cewa wata majiya a jam'iyyar PDP ta bayyana mata cewa don tabbatar da tsare-tsaren sa, kwanan nan Atiku ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a jihar Ribas.

An rahoto cewa Atiku ya mika hannun sulhu da goyon baya ga Wike, shahararren mai mulki a jam'iyyar PDP, don taimaka masa wajen samun karbuwa mai yawa, musamman a kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Rudani a Kano bayan majalisar jiha ta gayyaci shugaban alkalai kan shari'ar Rimingado

Atiku ya gana da gwamna Wike | Hoto: dailypost.ng

Majiyar daga PDP ta yi ikirarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasan ya nemi Wike ya yi aiki tare da shi kuma ya manta cewa bai goyi bayan sa ba a lokacin zaben 2019.

Wannan shiri na wuri da Atiku ya yi ya zo daidai da mummunan rikicin shugabanci a jam'iyyar PDP yayin da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar ke kira da a kori Uche Secondus, shugaban jam'iyyar na kasa kafin 2023.

Masoya Atiku a jihar Kano sun fara rabawa Kanawa burodi da sunan kamfe

Masoya ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, sun fara rarraba burodi, wanda ake wa lakabi da ‘Atiku Kawai’ ga mazauna Jihar Kano.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ake ikirarin cewa Atiku na neman tsayawa takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023, duk da cewa bai fito fili ya tabbatar da hakan ba, SaharaReporters ta ruwaito.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya fara neman mukamin mafi girma tun shekarar 1993.

Kara karanta wannan

Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi zabukanta na gunduma, Tahir

APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu

A wani labarin, Tshon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam'iyyun APC da PDP.

A cewarsa, wadannan jam'iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa 'yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.

Jega ya bayyana haka ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda Legit Hausa ta tattaro yana cewa, babu bukatar sake yin imani da jam'iyyun a nan gaba kasancewar sun gagara cimma wani abin kirki tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.