Abinda ya hana mu ceto daliban makarantar Tegina, Gwamnatin Neja
- Gwamnatin jihar Neja ta bayar da dalilan da zasu janyo bata lokaci wurin ceto daliban Islamiyyar Salihu Tanko a Tegina
- Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, ya bayyana yadda iyayen yara suka ki amincewa da amfani da sojoji wurin ceto yaran
- A cewarsa, gwamnatin jihar ta so tayi amfani da sojoji wurin ceto yaran amma iyayen suna tsoron garin hakan a cutar da yaransu
Minna, Niger - Gwamnatin jihar Neja ta bayar da dalilan da zasu iya janyo bacin lokaci wurin ceto yaran makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina.
Yayin da sakataren jihar, Ahmed Matane, yake tattaunawa da ThisDay a ranar Litinin, ya bayyana yadda iyayen yaran suka dakatar da amfani da sojoji wurin ceto yaran.
KU KARANTA: Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki
Iyayen dalibai ne suka hana amfani da sojoji
A cewarsa, gwamnatin jihar ta so amfani da sojoji wurin shiga dajin su bude wuta su ceto yaran amma iyayen yaran sun dakatar dasu saboda gudun rasa rayukan yaran garin yin hakan.
A cewarsa:
Gwamnatin jihar ta so amfani da sojoji su tafi da makamai har cikin daji amma iyayen yaran sun roki gwamnati don kada su rasa yaransu garin karon batta.
Sun rokemu kuma sun bukaci a yi amfani da hanyar sasanci don ceto yaransu shiyasa muka dakata.
Kun san irin wannan aikin zai iya janyo tashin hankali saboda kowa ya san ‘yan bindiga suna lura da yawonmu.
Gwamnati za ta biya kudin fansa don ceton dalibai
Sakataren ya gabatar da tsarin gwamnati na ba za su iya biyan ko sisi ba don sallamar ‘yan ta’adda ba don su ji dadin siyan makamai suna cutar da al’umma.
Matane ya bayyana yadda gwamnati da kanta take kokarin kawo karshen ta’addanci don yanzu haka akalla ana shirin kara sojoji 1000, ‘yan sanda da ‘yan sa kai don su kawo karshen rashin tsaro.
A cewarsa, duk da dai gwamnatin tarayya ta samar da jami’an tsaro, gwamnatin jihar za ta dinga biyan jami’an tsaro kudade a kowacce rana.
KU KARANTA: Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe
IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu
Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya nada DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban bangaren binciken sirri na 'yan sanda (IRT).
Disu zai maye gurbin Abba Kyari, wanda ake zarginsa kan wata harkallar cin hanci da gagarumin dan damfarar yanar gizo da Amurka ta cafke, Ramon Abbas.
Frank Mba, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Najeriya yace an nada Disu a wata takarda da ya fitar.
Asali: Legit.ng