Da duminsa: IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu

Da duminsa: IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu

  • IGP Usman Alkali Baba, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, ya nada Tunji Disu domin maye gurbin Abba Kyari
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, Frank Mba ya sanar a wata takarda da ya fitar
  • Wannan al'amarin na zuwa ne washegarin da Baba Alkali ya dakatar da Abba Kyari sakamakon binciken da za a fara kansa

FCT, Abuja - Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya nada DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban bangaren binciken sirri na 'yan sanda (IRT).

Disu zai maye gurbin Abba Kyari, wanda ake zarginsa kan wata harkallar cin hanci da gagarumin dan damfarar yanar gizo da Amurka ta cafke, Ramon Abbas.

Frank Mba, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Najeriya yace an nada Disu a wata takarda da ya fitar.

KU KARANTA: Ali Kachalla: Waye Hatsabibin shugaban 'yan bindigan Zamfara da ya harbo jirgin NAF

Kara karanta wannan

Tunji Disu: Abubuwa 8 da ya dace a sani game da magajin Abba Kyari a tawagar IRT

Da duminsa: IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu
Da duminsa: IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu
Asali: Original

KU KARANTA: Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe

Me takardar tace?

Kamar yadda takardar da aka fitar ta bayyana:

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba a yau, 2 ga watan Augusta ya amince da aike DCP Tunji Disu a matsayin sabon shugaban bangaren 'yan sandan binciken sirri (IRT).
Wannan ya biyo bayan hukuncin hukumar ne na maye gurbin shugabancin IRT tare da sake tabbatar da kwazon bangaren domin ayyukan da suka dace
IGP ya canja shugaban bangaren IRT domin kwatanta kwarewa da kwazo a bangaren shugabancin sashin. Ya tabbatarwa da 'yan kasa cewa IRT za ta cigaba da sauke nauyin dake kanta kamar yadda dokokin kasa da na duniya suka tanadar.

Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe

Idan da Abubakar Hassan ya san al’amarin da zai faru dashi da bai amince da zama ba a gidan da aka bashi ya zauna a Red Bricks, wani bangare na Damaturu babban birnin jihar Yobe. Hassan bai wuci watanni 6 ba a gidan kawai wani yazo ya kashe shi.

Kara karanta wannan

Hotunan motoci da suturun alfarma da kanin Abba Kyari ke fantamawa ciki

Abokai, ‘yan uwa da masoyan mamacin har yanzu suna cikin mamakin faruwar lamarin a ranar 22 ga watan Yulin 22 na 2021.

Maryam Salihu, ‘yar uwar mamacin ta tabbatar wa da Daily Trust cewa an dade ana jan kunnensa akan abota da Umar Shaibu, wanda aka fi sani da Abba, wanda aka fi zargi kuma ya yi alkawarin daina alaka dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel