Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

  • Wasu mayaƙan kungiyar ISWAP sun farmaki jerin gwanon sojoji ba zato ba tsammani a jihar Borno
  • Rahotanni sun bayyana cewa sojojin na kan hanyarsu na zuwa ɗakko wasu yan siyasa ne a Gobio
  • Sojoji da dama sun samu raunuka, amma har yanzun rundunar soji ba ta ce komai ba game da harin

Borno:- Gwamman yan ta'addan ISWAP sun yi wa jerin gwanon sojoji kwantan bauna suka bude musu wuta a hanyar Gubio/Damasak ranar Asabar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Adadi mai yawa da ba'a tantance ba na sojoji sun ji muggan raunuka a harin yayin da yan ta'addan suka yi awon gaba da wasu motocin sojojin.

Jami'an sojojin sun faɗa tarkon yan ta'addan ne yayin da suke kan hanyar zuwa Gobio domin ɗakko mambobin APC zuwa taronsu dake gudana a Damasak.

Tawagar Sojojin Najeriya
Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno Hoto: thisnigeria.com
Asali: UGC

Inda lamarin ya faru, Kareto shine mahaifar Bukar Gana Kareto, wanda ke wakiltar mazabun Kukawa/ Guzamala/Abadam/ Mobbar a majalisar wakilan tarayya.

Kara karanta wannan

El-Zakzaky da Matarsa na shirin fita daga Najeriya don ganin Likita

An yi watsi da garin na Kareto tsawon shekaru saboda ayyuakan ta'addanci na yan Boko Haram da ISWAP.

Ina sojojin zasu kafin faɗawa tarko?

Jami'an sojojin na kan hanyarsu na zuwa domin raka yan siyasa daga Abadam zuwa Damasak, inda taron jam'iyyar APC ke gudana.

Duk da cewa ƙaramar hukumar Abadam na cikin yankunan da basu shiguwa ta daɗi tun 2014, yan siyasa na gudanar da tarukansu a Damasak.

Amma wannan harin na yan ta'adda bai barsu sun samu halartar taron ba a wannan karon, inda suka koma Gubio.

Har yanzun hukumomi a rundunar sojojin ƙasa ba su maida maratani game da wannan harin ba.

A wani labarin kuma Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Caccaki Gwamatin El-Rufa'i, Sun Fadi Makudan Kudin da Suka Biya

Marcus Angwa, ɗaya daga cikin iyayen da aka sace yayansu a makarantar Bethel Baptist Kaduna, yace shi da yan uwansa sun koma ga Allah domin ya kuɓutar musu da yayansu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yiwa yan sanda biyu yankan rago, sun bankawa ofishinsu wuta

The Cable ta ruwaito cewa yan bindigan sun sace ɗalibai 121 daga gidan kwanansu a a makarantar Bethel Baptis ranar 5 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel