Cikakken Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Kubutar da Matar Kwamishina da Aka Sace

Cikakken Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Kubutar da Matar Kwamishina da Aka Sace

  • Gwarazan yan sanda sun ragargaji yan bindiga uku yayin da suka kubutar da matar kwamishinan Benuwai
  • Gwamna Ortom ya yi jinjina ga IGP ta tawagarsa na jihar Benuwai bisa wannan nasara
  • Ortom ya bada umarnin rushe gidan da masu garkuwan suka yi amfani da shi nan take

Benue:- Gwarazan yan sanda sun ragargaji masu garkuwa uku yayin da suka kubutar da matar kwamishinan jihar Benuwai da aka sace.

The Nation ta ruwaito cewa yan sanda sun kuɓutar da matar kwamishinan ƙasa, Ann Unenge, a wani operation da suka fita ranar Litinin 2 ga watan Agusta.

Bayan samun nasarar kuɓutar da Unenge, jami'an yan sandan sun tafi da ita hedkwatar rundunar yanda ta jihar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Matar kwamishina, Ann Onenge
Da Dumi-Dumi: Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Kubutar da Matar Kwamishina da Aka Sace Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jami'an yan sanda na Operation Zenda a jihar Benuwai sune suka jagoranci kuɓutar da Mrs. Ann Unenge, matar kwamishinan ƙasa.

Rahoton dailytrust ya nuna cewa matar tare da direbanta sun samu raunuka yayin musayar wuta tsakanin yan sanda da ɓarayin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An dage zaben kananan hukumomi na jihar Kaduna, an saka sabuwar rana

Mazauna yankin sun yi tururuwa hedkwatar yan sanda domin ganin gawarwakin waɗanda aka kashe.

Ortom ya yabawa IGP da jami'ansa

Gwamna Ortom na jihar Benuwai, wanda ya jagoranci wasu mambobin gwamnatinsa zuwa hedkwatar yan sanda, ya yabawa sufetan yan sanda na ƙasa da kuma jami'ansa dake jihar Benuwai.

Gwamna Ortom yace:

"Yan sanda sun nuna matukar kwarewa wajen fafatawa da yan bindigan bayan sun binciko maɓoyarsu."
Muna godiya sosai ga waɗanda suka yi kasadar taimakawa da sahihin bayani game da maɓoyar ɓarayin wanda hakan ya bada nasarar kuɓutar da matar da direbanta."
Wane mataki gwamnan ya ɗauka?

Gwamnan ya bada umarnin rushe gidan da yan bindigan suka yi amfani da shi nan take bisa dokar garkuwa da mutane ta jihar.

A halin yanzun, Kakakin hukumar yan sanda ta jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, yace bada jimawa ba za'a baiwa manema labarai cikakken bayanin abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

A wani labarin kuma Ba Da Jimawa Lamarin Yan Gudun Hijira Zai Zama Tarihi a Jihar Borno, Gwamna Zulum

Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa ba da jimawa ba lamarin yan gudun hijira zai zama tarihi.

Zulum ya faɗi hakane yayin wata ziyara da yakai sansanin yan gudun hijira dake Marte ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel